Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa sun kama wani kaka mai shekaru 75, Nnanna Felid, da wasu kanne biyu, John Abugu mai shekaru 43 da Kenneth Abugu mai shekaru 31, a wani samame daban-daban na yaki da miyagun kwayoyi.
An kama ‘yan’uwan Abugu ne a ranar Alhamis a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a Legas yayin da suke yunkurin shiga jirgi zuwa Indiya.
- Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya
- Sin Za Ta Kara Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar Zuwa 125%
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce an kama wadanda ake zargin dauke da hodar iblis mai nauyin kilo biyar da aka boye a bangon akwatunansu.
Ya ce sun yi ikirarin yin balaguro ne don neman magani amma an kama su ne sakamakon sahihan bayanan sirri.
Babafemi ya ce, “An kama ‘yan’uwan biyu ne a filin jirgin saman Legas a ranar Alhamis, 3 ga Afrilu, 2025, biyo bayan binciken da aka yi na sahihan bayanai, sun yi ikirarin cewa suna tafiya Indiya ne domin neman lafiya, amma da jami’an NDLEA suka yi bincike sosai a kan akwatunansu, daga baya aka gano wata hodar iblis a bangon jakunkuna.”
A wannan rana a filin jirgin saman Legas, Babafemi ya ce jami’an ‘yansanda sun kama wata ‘yar asalin kasar Ghana mai shekaru 20, mai suna Parker Darren Hazekia Osei, mai shekaru 20 da haihuwa, dauke da fakiti 36 na Loud—wani nau’in tabar wiwi mai karfin gaske, a cikin wata katuwar jakar tafiya mai nauyin kilogiram 19.40.
Ya ce wanda ake zargin wanda ya bayyana kansa a matsayin dalibin Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar Gabashin Landan, ya taso ne daga birnin Bangkok na kasar Thailand ta hanyar jirgin Ethiopian Airlines, ya kuma amince ya dauko kayan a Bangkok domin kai wa Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp