Ɗan wasan gaban Wolves, Tolu Arokodare, ya zama gwarzon wasan da Nijeriya ta doke Rwanda da ci ɗaya a wasan neman gurbin zuwa Kofin Duniya.
Arokodare, wanda aka shiga wasan a matsayin canji, ya ci ƙwallo a minti na 51, bayan samun dama a cikin da’ira ta 18.
- Babban Taron MDD Ya Zartas Da Kudurin Hadin Gwiwar MDD Da SCO
- Boko Haram Ta Hallaka Mutane 61 A Jihar Borno
Wannan nasara ta ɗaga Nijeriya zuwa matsayi na uku a rukuni C da maki 10, yayin da Rwanda ta koma matsayi na huɗu da maki takwas.
Ɗan wasan gaban Super Eagles, Victor Osimhen ya ji rauni minti na 10 kafin tafiyar hutun rabin lokaci.
Afirka ta Kudu, wadda ke na ɗaya da maki 16, ita ce za ta karɓi bakuncin Nijeriya a wasan gaba a Bloemfontein a ranar Talata, wanda ake ganin wasan mai zafi ne.
Wasanni uku ne kacal suka rage a rukunin.
Ƙasar da ta fi kowa maki a ƙarshen zagaye ita ce kawai za ta je gasar Kofin Duniya da za a yi a Amurka, Mexico da Canada.
Saboda haka, dole ne Nijeriya ta doke Afirka ta Kudu don cikar burinta.














