Neymar ya zarce Pele a matsayin dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a raga ga kasar Brazil bayan ya jefa kwallaye biyu a wasan da suka doke Bolivia da ci 5-1.
Kwallayen da Neymar ya jefa, yasa ya jefa kwallo 79 jimilla inda ya zarta Pele da kwallo biyu.
Dan wasan mai shekaru 31, wanda ya buga wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ya zarce fitaccen dan wasa Pele a wadanda suka fi zura wa Brazil kwallaye.
Ban taba tunanin karya wannan tarihin ba, ban fi Pele ko wani dan wasa ba a tawagar kasar, in ji Neymar.
Pele, wanda ya mutu a watan Disamba yana da shekaru 82, ya ci kwallaye 77 a wasanni 92 tsakanin 1957 zuwa 1971.
Ana yi masa kallon daya daga cikin manyan shahararrun yan wasan kwallon kafa da suka taba buga wasan.
Neymar ya zama dan wasa mafi tsada a duniya lokacin da ya koma Paris St-Germain daga Barcelona kan fan miliyan 200 a shekarar 2017.
Ya bar kungiyar ta Faransa a lokacin bazara don komawa kungiyar Al-Hilal ta Saudi Pro League.