Rahotannin da ke fitowa daga Jamhuriyar Nijar na nuni da cewa gwamnatin mulkin soja a kasar ta fara kame jami’an gwamnati da suka hada da ministan ma’adinai na jam’iyya mai mulki, da kuma ministan mai Mahamane Mahamadou, wanda kuma dan tsohon shugaban kasar, Issoufou Mahamadou ne.
Ministoci akalla hudu ne da suka hada da tsohon minista da kuma shugaban jam’iyyar hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ne, aka kama a hannun gwamnatin soja da ta kwace mulki a ranar 26 ga watan Yuli, in ji jam’iyyar a ranar Litinin.
- Ba Abin Da Zai Hana Mu Shiga Zanga-Zanga —NLC
- A Guji Tarzoma Yayin Zanga-zanga, IGP Ya Gargadi NLC Da TUC
“Bayan an tsare shugaban kasar a makon da ya gabata, sojojin sun sake tsare wasu,” in ji jam’iyyar Democratic Democratic Party (PNDS) a cikin wata sanarwa.
“A safiyar ranar Litinin, an kama ministan mai, Mahamane Sani Mahamadou, dan tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou da kuma ministan ma’adinai Ousseini Hadizatou,” in ji sanarwar.
An kuma kama shugaban kwamitin zartarwa na PNDS na kasa, Fourmakoye Gado, in ji shi.
A baya dai gwamnatin mulkin sojan kasar ta kama ministan harkokin cikin gida Hama Amadou Souley da ministan sufuri Oumarou Malam Alma da kuma Kalla Moutari dan majalisa kuma tsohon ministan tsaro, in ji jam’iyyar.
Jam’iyyar ta yi kira da a sake su cikin gaggawa, tana mai cewa Nijar na cikin tsaka mai wuya.
Wata majiya da ke kusa da fadar shugaban kasar ta ce an kuma kama ministan koyar da sana’o’i, Kassoum Moctar.
Kamen ya zo daidai da wata sanarwa da gwamnatin mulkin sojan kasar ta bayar na bukatar “dukkan tsofaffin ministoci da shugabannin hukumomi da su mika motocin ofishinsu.
A ranar Larabar da ta gabata ne wasu jami’an tsaron fadar shugaban kasar suka hambarar da gwamnatin shugaba Bazoum, wanda shugabansu Abdourahamane Tiani, ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasar.
Sai dai ECOWAS da Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah-wadai da juyin mulki da sojojin suka yi.
Inda suka ba su wa’adin mako guda don dawo da mulki ga shugaba Bazoum.