Connect with us

NOMA

Nijeriya Na Burin Samun Ninkin Kasafinta Sau Hudu Daga Manja A 2021 

Published

on

Alkaluma sun nuna cewa, Nijeriya nan da shekara ta 2021, farashin Manja a kasuwar duniya a na sa ran zai kai Dala biliyan 92.84 daidai da Naira tiriliyan 33, inda hakan ya kai kusan sau hudu na kasafin kudin Nijeriya Naira tiriliyan takwas biyo bayan annobar cutar Korona, wacce ta baddala al’amuran tattalin arziki a 2020.

Wannan alkaluman suna kunshe ne a cikin rahoton bincike na kasuwar Zion, inda kuma a biasa fashin bakin da akayi na duniya a shekarar 2015 zuwa shekarar 2021, an nuna cewa, kasuwar ta karu a duk shekara da kashi 7.2 daga dala biliyan 65.75 zuwa dala biliyan 92.84 a shekarar 2020.
Bugu da kari, Nijeriya ta kai mataki na biyar a duk shekara wajen samar da manja da ya kai tan-tan 904,000, inda kuma take bin kasar
Indonesiya dake samar da tan-tan miliyan 33.4 sai kuma kasar Malaysiya tana samar da tan-tan miliyan 19.9, haka kasar Thailand tan samar da tan-tan miliyan 1.8m sai kuma kasar Colombia da ta ke samar da tan-tan miliyan 1.2.
Hakan ya kuma nuna cewa, kasar Indonesiya da kuma kasar Malaysiya tana samar da kimanin kashi 85 bisa dari na Manja a duniya.
Amma kasar Malaysiya, wadda ta kasance daga cikin ta daya dake samar da Mnaja, ta kasance tana a bayan Nijeriya a shekarar 1960.
Cigaban kasar Malesiya, yaci gaba da karauwa, inda hakan ya hanifar da gasa kana yin watsi da fannain da Nijeriya ta yi, inda ta mayar da hankailin ta kachokam kan man fetur.
A yanzu haka, bukatar da Nijeriya take dashi na Mnaja, ya kai kimain tan-tan 2.5, inda Nijeriya a yanzu, take iya samar da kimanin tan-tan na Manjan day a kai kimanin tan-tan 1, inda hakan ya sanya aka samu gibin tan-tan 1.5.
A kwannan baya ana ruwaito Gwamnna Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele ya sanar da cewa, Babban Bankin na Nijeriya CBN, zai zuba kimanin naira biliyna 30 a fannin yadda za a kara samar dashi da ywa a kasar nan.
Gwamnna Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele ya sanar da cewa, nufin mu shine, don mu tabbtar da an nuna kimanin kadada miliyan 1.4 ta Kwakwar Manja a cikin shekaru uku masu zuwa.
A cewar Gwamnna Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, don cimma wannan burin, Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya gana da gwamnonin jihohin kasar nan sha 14, inda kuma suka yi alkwarin samar da kadada 100,000 a jihohinsu.
A karshe, Gwamnna Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele ya sanar da cewa, kafin Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin a garkame iyakokin Nijeriya na kan tudu, Nijeriya ta na kasshe kimanin dala miliyan 500 duk shekara wajen shigo da Manja cikin kasar nan.
Advertisement

labarai