Yayin da aka sake samun bullar kwayar cutar Ebola samfurin Sudan a Uganda, cibiyar hana yaduwar cututtuka da maganinsu ta kasa, ta bayyana cewar akwai yiyuwar Nijeriya ta sake fuskantar shigowa da bullar cutar Ebola.
Shugaban cibiyar NCDC Dokta Ifedaya Adetifa, shi ne ya bayyana haka a wani bayanin da aka fitar jiya cewa da akwai yiyuwar sake bullar cutar Ebola a Nijeriya, yawan tarukkukan da ake yi masu nasaba da siyasa.
- Ya Yi Yunkurin Jefa Matarsa Rijiya Don Zargin Tana Cutarsa
- Mauludi: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar 10 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Hutu
Shi yasa bikin kirsimatai mai zuwa da sauran bukukuwa na addinai wadanda za a yi a watannin da suka rage a wannan shekarar 2022.
Ya ba da sauran dalilan da suka hada da cewar “ita samfurin kwayar cutar Ebola ta Sudan yanzu ba ta da magani, ko wani lasisi da aka yarda da samar da allurar maganin rigakafin cutar.
Ita samfurin cutar Ebola ta Sudan ta bambanta ne daga kashi 41 zuwa100 a barkewar cutar daban- daban da aka samu.
“Yiyuwar sake bullar cutar tana da karfi saboda yawan zirga- zirgar da ake yi tsakanin Uganda Nijeriya, ba ma kamar ta tasahr Jirdin sama ta Kenya da ke babban birnin kasar Nairobi.
Ita tasahar ta Nairobi ta kasance wata tasha ce ta wancan sashen da kasashen da ta ke makwabtaka da su ka hada iyaka ta kai tsaye da kasar Uganda.
Sai dai kuma duk da hakan Ifedayo ya ce Nijeriya tana da dukkan abubuwan da suka kamata na fasaha, da yawan ma’aikatan kula da lafiya, wuraren gwaji, domin fuskantar cutar ko da ace ta bulla.
Ya ce ana iya tunawa da nasara da Nijeriya ta samu lokacin da cutar ta bulla a shekarar 2014, ga kuma irin ci gaban da aka samu, ta bangaren yadda za a fuskanci cutar wadda ta barke cikin gaggawa, kamar lokacin da aka fuskanci annobar cutar Korona.
Ya ci gaba da bayanin cewa“ Muna da kayayyakin gwajin cutar a dakin gwaji na kasa a Abuja da kuma Asibitin koyarwa na Jami’ar Legas inda ake da wata babbar cibiya ce da take dakin gwaje- gwajen gano musabbabin kamuwa da cuta’’.
Bugu da kari Shugaban cibiyar wurin binciken da ke da shi za a kara ingantashi da sauran dakunan gwaje- gwaje da suke a Birane, inda za a lura da muhimmin wurin da ake shigowa kasa, da kuma duk abubuwan da za a bukatana aikin.
Hukumar lafiya ta duniya ta tabbatar da barkewar cutar a kasar Uganda, duk wannan al’amarin cutar yana faruwa ne ta hanyar samfurin Ebola na Sudan, wanda yayi sanadiyar barkewar cutar a Uganda Sudan ta Kudu, da kuma jamhuriyar kasar Damukuradiyya ta Congo.
Cibiyar bincike da kasar Uganda ta tabbatar da an samu wani matashi mai shara 24 bayan da aka gwada wadansu abubuwan da ake amfani da su lokacin gwaji, ya nuna alamun kamuwa da cutar wanda daga baya kuma ya mutu.
Wannan al’amarin ya faru ne a gundumar Mubendea tsakiyar babban birnin kasar da ke na nisan kilomita 175 daga Kamfala. Ya zuwa ranar 29 ga Satumaba ma’aikatar lafiya ta kasar Uganda ta ba da labarin an gwada mutane 54 (35 an tabbatar da sun kamu da cutar, yayin ake da shakku da19) mutane 25 sun mutu.
Sai kuma wasu mutane 7 da aka tabbatar da sun kamu da 18 wadanda ake shakku akan su. Ma’aikatar lafiya ta Uganda tare da taimakon hukumar lafiya ta duniya, suna aiki tare ta ganin an kawo karshen cutar da yaduwarta, kamar dai yadda cibiyar ta NCDC ta bayyana.