Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta bude wani ofishin bayar da fasfo inda masu neman fasfo cikin hanzari za su iya samu cikin kwana daya rak, bayan sun gabatar da bukata ga hukumar.
Ofishin wanda aka bude a Unguwar Maitama da ke Abuja, na hadin gwiwa ne a tsakanin NIS da Kamfanin Sadarwar Zamani na Iris Smart Technology Ltd. Har ila yau, ofishin ya kunshi sashen bayar da lambar dan kasa ta Hukumar NIMC ga masu neman fasfo kawai , da mazaunin manyan baki, da ihsanin dan abin sha, da tsara bin layi cikin sauki da sauran abubuwa na inganta walwala da samun biyan bukata ta fasfo.
Da yake jawabin maraba a yayin bude ofishin, Shugaban NIS, CGI Muhammad Babandede ya yi bayanin cewa an bude ofishin ne domin ya taimaka wajen shawo kan kalubalen da ‘Yan Nijeriya ke fuskanta yayin da suke neman fasfo cikin hanzari a cikin gida da waje.
Don haka ya ce an kafa ofishin samun fasfo ciki hanzari na Maitama ne domin cimma bukatun wadanda suke da muradin biyan kudi na musamman don samun fasfo cikin hanzari da gamsuwa.
Sai dai kuma, Babandede ya ce abubuwan da suka shafi sauya bayanin mai neman fasfo, da maye gurbin fasfon da ya lalace ko ya bace ko aka sace, ba su daga cikin ayyukan da za a rika yi a ofishin na Maitama, sai dai a shalkwatar hukumar da sauran ofisoshin fasfo da aka amince.
Bugu da kari ya yi albishir ga masu neman fasfo cewa a halin yanzu akwai wadataccen littafin fasfo a kasa kuma ana ci gaba raba rabawa ga dukkan cibiyoyin hukumar na bayar da fasfo. “Saboda haka muna rokon masu neman fasfo su kara hakuri kadan domin bai wa ofisoshin fasfo damar kammala sallamar wadanda suka riga zuwa.” In ji shi.
Dangane da kudin da za a biya na yin fasfon a ofishin na Maitama, CGI Babandede ya ce, “Muna sake tunatar da jama’a cewa kar su biya kudin fasfo ko wasu takardu da ayyuka na NIS a ko ina idan ba ta shafin intanet ba ko kuma wasu bankuna da aka zaba aka jero sunayensu a adireshin hukumar na shafin intanet www.immigration.gov.ng.
“Wannan cibiyar ta bayar da fasfo cikin hanzari za ta rika cajar karin Naira dubu ashirin (20,000) ga wadanda suke son fasfo cikin kwana uku ko kuma karin Naira dubu talatin ga wadanda suke son samu cikin kwana guda daya rak (awa 24). Kar mutane su yarda su yi hulda da ‘yan bayan fage, akwai wurin neman karin bayanin duk abin da mutum yake so a shafinmu na intanet da yake aiki dare da yini, mutum zai iya amfani da shi wajen neman bayani ko kai rahoton duk wata kumbiya-kumbiya domin hukumar ta dauki mataki nan take”.
Ya yi gargadi ga jami’an da za su yi aiki a ofishin su tabbatar da gaskiya da rikon amana, domin hukumar ba za ta yi wata-wata ba wajen hukunta duk wanda aka kama yana sakaci da aiki ko aikata ba daidai ba kamar yadda ta yi ga jami’an da ke ofishin bayar da fasfo na Amana, a makon da ya gabata
CGI Babandede ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa goyon bayan da yake bai NIS ta fuskar sauye-sauye masu ma’ana da take aiwatarwa, yana mai cewa, “a ranar 4 ga watan Maris, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari GCFR ya kaddamar da katafariyar cibiyar fasahar sadarwa ta zamani wadda tuni ta fara amfanarwa ga sashen tsaron kasar nan da kuma kara wa kasar kima da martaba a idanun duniya da sauran alfanu masu daman gaske.”

Haka nan ya jinjina wa Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola bisa kwazonsa na tabbatar da cewa NIS ta kasance hukumar shige da fice mafi kwarewa a sahun takwarorinta na duniya.
Babandede ya nanata cewa NIS ba za ta sarara ba a kokarin da take yi na zama hukumar shige da fice da ta tsere-wa-tsara a duk fadin duniya.
A nashi bangaren, Ministan Cikin Gida Aregbesola wanda ya kaddamar da ofishin, ya ce gwamnati ba ta kara kudin fasfo a ofishin ba, karin da za a biya ladan aiki ne na kamfanin da aka yi hadin gwiwa da shi.
Ya ce an samar da ofishin na Maitama ne bisa amfani da umarnin bangaren zartaswa a kan saukaka hada-hadar kasuwanci a cikin kasa da samar da aikin yi ga ‘yan kasa domin rage fatara, kasancewar bakidayan wadanda za su yi aiki a ofishin ‘Yan Nijeriya ne.
Aregbesola ya kuma yi amannar cewa ofishin na Maitama zai rage wahalhalun da ake fuskanta wajen neman fasfo a cibiyoyin fasfo da ke fadin kasar nan, “sannan daga yanzu mun huta da masu neman alfarma da ke bugo waya suna neman a yi musu fasfo cikin hanzari.”
Ministan ya yaba wa shugaban NIS CGI Babandede bisa namijin kokarinsa a shugabancin NIS, yana mai cewa sun kaddamar da ayyuka na ci gaba daban-daban a hukumar a karkashinsa.
Haka nan ya yi kira ga jami’an NIS su kara shan damara wajen aikin kula da iyakokin kasa wanda ya ce ba karamin jan aiki ba ne.
Daga bisani dai daya daga cikin kwastamomin da aka yi wa fasfon, ta yi bayani mai gamsarwa kan yadda ta samu fasfonta cikin hanzari ba tare da walankeluwa ba.