Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP) a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, Mista Peter Obi, da wasu jiga-jigan jam’iyyar, sun isa cikin kotun koli da ke sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ke Abuja, domin ganin yadda za ta gudanar da shari’ar zaben a ranar Laraba.
Obi ya samu rakiyar shugaban jam’iyyar na kasa Mista Julius Abure da Sanata Victor Umeh da sauran jiga-jigan jam’iyyar.
Yayin zaman kotun a yau Laraba, ana sa ran kotun za ta yanke hukunci kan bukatar da lauyan hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ya shigar na neman kotun da ta sauya hukuncinta da ta baiwa jam’iyyun PDP da LP na duba kayayyakin zaben da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Lauyoyin Atiku da PDP, Joe-Kyari Gadzama, SAN, Mike Ozekhome, SAN, Emeka Etiaba, SAN, da dai sauransu, duk sun halarci kotun.
Onyinyechi Ikpeazu, Onyinyechi Ikpeazu, SAN da Alex Ejesieme SAN, da Alex Ejesieme, SAN, sune ke wakiltar Obi da LP yayin da Omosanya Popoola, da Akintola Makinde ke wakiltar Tinubu da APC, yayin da Tanimu Inuwa, SAN shine lauyan INEC kan lamarin.
Har yanzu dai kotun ba ta fara zama ba a lokacin rubuta wannan rahoton.
Cikakkun bayanai Daga baya…