Muhammad Awwal Umar" />

PDP Ga Gwamnatin Neja: Ku Bayyana Yadda Ku Ka Kashe Bashin Dala Miliyan 181 Na Aikin Hanyar Bida

Tsohon gwamnan Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu ya zargin gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello da yin awon gaba da bashin da ya karbo dan yin aikin tagwayen hanyar Minna zuwa Bida da ya karbo daga bakin musulunci. Islamic Debelopment Bank ( IDB). Tsohon gwamnan yayi zargin ne a sakatariyar jam’iyyar PDP lokacin kaddamar da ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi da hukumar zaben jihar ta shirya gabatar wa a karshen watan Nuwamba mai kamawa.

Tsohon gwamnan yace an karbo wannan bashin ne dan aikin tagwayen hanyar Minna zuwa Bida kuma kudin sun shiga aljihun gwamnatin jiha a lokacin da yake gab da barin ofis. Indai ba a manta ba gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello ta bayyana wannan aikin a cikin kasafin kudinta na shekarar da ta gabata wanda har yanzu ko bulo ba a dora ba balle a ga alamar aikin a zahiri.

Tsohon gwamnan ya bayyana mamakin sa akan yadda gwamnatin APC a Neja ke karkatar da kudaden da aka ware dan yin aiki akan wasu bukatu na daban, inda ya bayyana cewar lokaci yayi da jama’ar jihar zasu farka daga dogon baccin da suke yi dan sanya ido akan yadda ake kokarin kashe jihar bisa son zuciya. Ya cigaba da cewar maganar lalacewar hanyoyin jihar nan sakacin gwamnatin jiha ne wanda ba ta dauki ayyukan raya jihar da muhimmanci ba.

Dakta Mu’azu Babangida, yace da kaina na tafi Jidda dan nemo wannan bashin kuma an amince min, lokacin da kudin suka shigo na bar kujerar a shekarar 2015, kuma a kasafin kudin 2016 gwamnatin APC ta sanya shi amma abin mamaki har yanzu ba mu san inda wannan kudin ya shiga ba.

Dan haka akwai bukatar jama’ar jihar su binciki inda aka kashe kudaden da kuma dalilin karkatar da su.

“ Ina da tambaya ga wannan gwamnatin, shin ina kudin suke kuma me aka yi da su. Ya kamata su fito su yi bayani kuma su bayyana mana yadda suka yi da kudin.

Dakta Babangida Aliyu, ya nemi jama’ar Neja da su zabi ‘yan takarkarun PDP a matakin kananan hukumomi, inda ya bayyana cewar zaben PDP ne zai baiwa jama’a damar samun walwala da samar da gwamnati mai inganci wanda zai alfanu kasa da jama’ar ta, ta fuskar cin ribar mulkin dimukuradiyya a jihar.

Taron dai ya samu halartar manyan jami’an PDP a kasa da jihar Neja. Cikinsu har da tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya zama babban bako a taron.

Da yake bayani bayan mika tutar PDP ga ‘yan takarar su ashirin da biyar na shugabancin kananan hukumomin. Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana mamakin sa kan rashin kammala aikin hanyar Suleja zuwa Minna, wanda yace an faro tun lokacin mulkin Goodluck Jonathan.

Inda yace ya zama wajibi ga gwamnati ta mayar da hankali wajen ayyukan raya kasa da zasu anfani jama’a, domin siyasar aikin hanya da ruwan sha lokacin yayinsa ya wuce zuwa yanzu ya kamata duk wata hanya ta anfanin jama’a ya kamata an kammala shi domin gwamnati na da kudin wadannan abubuwan, amma abin mamaki jihar Neja da ke da hanyoyin samun kudade a ce hanya ma ta gagare ta wanda wannan ba karamin koma baya ba ne ga jihar nan.

Honorable Danladi Tambaya, mataimakin dan takarar shugabancin karamar hukumar Kontagora yace ba jihar da gwamnatin APC ta mayar baya kamar jihar Neja, domin alkawurran da suka yi a lokacin yakin neman zabe har yanzu ko kashi biyar cikin dari ba su samar ba, illa kullun kirkiro abubuwan da zasu muzanta rayuwar talakan jihar.

Ba mu da hanyoyi tun daga kan gwamnatin jiha har na tarayya balle kuma a ce mu a matakin kananan hukumomi mu yi tunanin samun romon dimukuradiyya.

Mun fito kuma mun tsaya dan ceto jihar mu daga wannan halin na karayar tattalin arziki da ya same mu, dan haka ina jawo hankalin duk wani mai son cigaban jihar nan da ya tabbatar ya marawa jam’iyyar PDP a wannan zaben na kananan hukumomi mai zuwa.

Exit mobile version