PDP Na Zargin Gwamnatin Jihar Ebonyi Da Gallaza Wa ‘Yan Adawa A Jihar

PDP

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Jam’iyyar (PDP) tana zargin gwamnatin Jihar Ebonyi da amfani da kungiyar tsaro da ake kira da suna Ebubeagu wajen gallaza wa abokan adawa da kuma wadanda suke wasu bayanan rashin goyon baya ga gwamnatinsa.

Sai dai kuma ita gwamnatin Jihar ta bayyana cewar shi zargin da ake yi mata yana daga cikin wani shiri ne da ake son yin amfani da shi,wajen ganin an goga wa ita Gwamna Dabe Umah, kashin kaji, domina samar da wani yanayi na tayar dazaune tsaye a Jihar.

Domin kuwa wannan wani babban lauya ne Amos Ogbonna, wand aaka ceto shi daga wurin wadanda suka yi garkuwa da shi, bayan sun gallaza ma shi azaba, makon daya gabata, yanzu shi ne wanda yake cewar ai gwamnatin Jihar ce ta sa aka yi masa hakan.

Ya bayyana cewar gwamnatin Umahi a shirye take da ta takurawa abokan adawa da suke fadar gaskiya, da kuma yadda   al’amurra suke a zahirance.

Kamar dai yadda ya ce ba wata maganar da jam’iyyar PDP tayi, wadda shi gwamna Umahi  da mataimakansa, ba za su yi mata kallon wani al’amari daban ba,amma suna mantawa da ma’anar ko kuma abinda za a amfana da daga cikin ita mu’amalar.

Ya yi karin bayani da cewar “Wani abinda ya dace ayi misali da shi shi ne wani al’amarin da bai dade da faruwa ba, shi ne yadda aka gallaza ma wani mutum da ake kira da suna Ogbonna, wanda babban lauya ne, wanda kuma ake ganin gwamnatin Jihar ce ta sa wasu suka yi hakan.

Sun gallazawa Ogbonna na kwanaki ba tare da sun nuna jin tausayin sa ba, amma an godewa Allah da basu kai ga kashe shi ba.

“Wannan dam sauran wasu misalai suna nan. D aakwai wani abinda ba a dade da yin magana akan shi ba, shi ne akwai wani mutum wanda an ba shi dama har tayi yawa wato Ebubeagu  shi da ‘yan barandar shi, suna ci gaba ne da gallazawa abokan adawa na jam’iyyar gwamnan, da kum ayadda yake tafiyar da mulkin sa, a  wasu wurare, kamar dai yadda ya bayyana.”

Onu  ba kanshin wata gaskiyada ke nuna ita gwamnatin Jihar tana amfani ne da wata dama, wadda za su gallazawa abokan adawa, ba yadda za a basu damar kare kansu, ko kuma su bayya ra’ayinsu akan ita gwamnatin Jihar Ebonyi.

Amma kum ada yake fadar albarkacin bakin sa akan zargin da ake yi masu, kwamishine yada labarai da kuma wayar da kan al’umma na Jihar Eboyi, Mista. Uchenna Orji, ya bayyana cewar shi zargin da jam’iyyar PDP take yi, wannan wani abin takaici ne, wannan wani abu ne wanda aka bulla da shi ba domin komai ba, sai don a kawo wasu abubuwan da ba gaskiya ba. domin , aga cewar gwamnatin bata tsinanawa al’umma wani abu.

Ya ci gaba da bayanin “Mun sancewar an ware milyoyin Nairori kan yin wadansu abubuwan da basu da wani tasiri ga al’umma, da kuma amfani kafafen sadarwa na zamani, domin a nuna shi gwamnan ba wani banne, ba kuma abubuwan kirkin da yake yi, bayan kuma ga abubuwan ci gaban da yayi.

“Akan hujjojin da muke da su da akwai kanshin gaskiya da ke nuna cewar shi Ogbonna, daga karshe an gan shi da Linus Okorie da kuma Chidiebere Egwu wanda aka fi sani da ( Hulala). Don haka muna bukatar hukumomin tsaro, su dora alhakin abubuwan da suke faruwa a kan su, da kuma inda su abokan da suke taimaka masu suke, domin kuwa mu muna da manyan hujjojin da ba za a taba share su ba.

Exit mobile version