A jiya Juma’a, Madam Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta yi hira gami da shan shayi tare da Madam Elke Budenbender, uwargidan shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmerer, wadda take wa mijinta rakiya wajen ziyarar aiki a kasar ta Sin.
Yayin hirarsu, Madam Peng ta yi waiwaye kan yadda ta raka shugaba Xi Jinping ziyara a kasar Jamus a shekarar 2017, kana ta nuna yabo ga Madam Budenbender bisa kokarin da ta yi wajen kare hakkin mata da yara cikin dogon lokaci.
Ban da haka, matan shugabannin biyu sun kalli wani shirin bidiyon da ya shafi cudanyar al’umma, musamman ma a fannin al’adu, da ake yi tsakanin bangarorin Sin da Jamus, inda Madam Peng ta ce, akwai dimbin ayyukan hadin gwiwa masu alaka da aikin ilimi, da al’adu, da ake gudanarwa tsakanin kasashen 2. Ta kuma bayyana cewa, ana fatan ganin karuwar mu’amala tsakanin al’ummun Sin da Jamus, don karfafa fahimtar juna, da zumunta a tsakaninsu.
A nata bangare, Madam Budenbender ta gode ma Madam Peng kan yadda aka tarbe ta da wani yanayi da tsari masu gamsarwa, kuma ta ce yadda Madam Peng ke kokarin ba da gudunmowa wajen inganta cudanya da hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Jamus a fannin al’adu ya burge ta sosai.
Ban da haka uwargidan shugaban kasar Jamus ta bayyana niyyarta ta samar da taimako wajen karfafa hadin gwiwar da kasashen 2 suke yi a fannin kare hakkin mata da yara, da dai sauransu, da kara dankon zumunci tsakanin al’ummun bangarorin 2. (Bello Wang)














