ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 31, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mutane 38 Sun Kamu Da Wata Sabuwar Cuta Da Ba A Gano Irinta Ba A Zamfara

by Abubakar Sulaiman
3 hours ago

Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da samun mutane 38 da suka kamu da wata cuta da har yanzu ba a gano nau’inta ba a wasu yankunan jihar, lamarin da ya sa hukumomin lafiya tura tawagar gaggawa domin gudanar da bincike da daƙile yaduwarta.

Rahoton da Cibiyar Kula Da Ayyukan Gaggawa Kan Lafiyar Jama’a (PHEOC) na Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta fitar ya nuna cewa an samu mafi yawan masu fama da cutar ne a ƙaramar hukumar Shinkafi, yayin da aka samu ƙarin wasu da suka kamu da ita a Moriki, da ke ƙaramar hukumar Zurmi. An tattara waɗannan alkaluma ne zuwa ranar 29 ga Oktoba, 2026.

Ma’aikatar Lafiyar ta bayyana cewa waɗanda suka kamu da cutar na fama da zazzaɓi, da ciwon kai, da rashin sha’awar cin abinci, da amai, da ciwon gaɓoɓin jiki da kuma raunin jiki gaba ɗaya.

ADVERTISEMENT

Binciken farko da likitoci suka gudanar ya nuna yiwuwar cututtukan zazzabin cizon sauro, ko gastroenteritis (cutar da ke shafar ciki da hanji) ko sankarau ne ke haddasa matsalar, sai dai har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabinta ba.

Domin gano tushen cutar, gwamnati ta tura tawagar ƙwararrun ma’aikatan lafiya ƙarƙashin jagorancin Daraktan Kiwon Lafiyar Jama’a, Dakta Yusuf Abubakar. Tawagar na duba marasa lafiya a asibitocin Shinkafi da Moriki, tare da raba magunguna da kayan aikin jinya. Haka kuma, an tattara samfuran jinin da sauran bayanan marasa lafiyar domin gudanar da gwaje-gwajen a ɗakin bincike a Sakkwato.

LABARAI MASU NASABA

An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

Kwamishiniyar Lafiya ta jihar, Dakta Nafisa Maradun, ta shawarci mazauna yankunan da abin ya shafa da su garzaya asibiti da zarar sun fara ganin alamomin cutar. Ta kuma gargaɗe su kan guje wa shan magani da kansu ba tare da shawarar likita ba, tare da kira ga jama’a da su ba jami’an lafiya haɗin kai yayin da ake ci gaba da bincike.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su
  • Abubakar Sulaiman
    An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara
  • Abubakar Sulaiman
    Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin
  • Abubakar Sulaiman
    Ɗan Takarar Gwamnan Sakkwato Na ADC, Ya Tsallake Rijiya Da Baya

MASU ALAKA

An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara
Manyan Labarai

An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

October 31, 2026
Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara
Manyan Labarai

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

October 30, 2026
El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci
Manyan Labarai

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

October 30, 2026
Next Post
An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su

Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su

October 31, 2026
An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

October 31, 2026
Mutane 38 Sun Kamu Da Wata Sabuwar Cuta Da Ba A Gano Irinta Ba A Zamfara

Mutane 38 Sun Kamu Da Wata Sabuwar Cuta Da Ba A Gano Irinta Ba A Zamfara

October 31, 2026
Peng Liyuan Ta Yi Hira Da Uwargidan Shugaban Kasar Jamus

Peng Liyuan Ta Yi Hira Da Uwargidan Shugaban Kasar Jamus

October 31, 2026
Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin

Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin

October 31, 2026
Yadda Talauci Ya Sa Mutane Komawa Amfani Da Magungunan Gargajiya

Yadda Talauci Ya Sa Mutane Komawa Amfani Da Magungunan Gargajiya

October 31, 2026
Ɗan Takarar Gwamnan Sakkwato Na ADC, Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Ɗan Takarar Gwamnan Sakkwato Na ADC, Ya Tsallake Rijiya Da Baya

October 31, 2026
Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Dakile Kamfanonin Hada-hadar Sadarwa Na Kasar

Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Dakile Kamfanonin Hada-hadar Sadarwa Na Kasar

October 30, 2026
Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Switzerland

Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Switzerland

October 30, 2026
Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

October 30, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.