A yau Jumaa 30 ga wannan wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban kasar Switzerland Guy Parmelin a birnin Beijing, yayin da mista Parmelin din ke ziyarar aiki a kasar Sin .
A yayin ganawar, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, bisa yanayi na tinkarar nuna raayin bangare daya, da ba da kariyar cinikayya, gudanar da ciniki da hadin gwiwa cikin yanci ya kasance muhimmin aiki, yayin da ake raya dangantaka tsakanin Sin da Switzerland, kuma hakan ya shaida cewa, kasashen biyu sun yi imani, da kiyaye bude kofa ga kasashen waje, da yin hadin gwiwa da juna, tare da taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya mai bude kofa.
Kazalika, kasar Sin tana son yin kokari tare da Switzerland wajen kara bude kofa, da yin hadin gwiwa, da sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya, ta yadda za a tabbatar da raya hadin gwiwar tattalin arziki, da cinikayya a tsakanin Sin da Turai, da ma raya tattalin arzikin duniya baki daya.
A nasa bangare kuwa, shugaba Parmelin cewa ya yi, shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 10 da kulla sabuwar dangantakar abokantaka, bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Switzerland da Sin, kuma kasashen biyu sun kammala shawarwarin kyautata yarjejeniyar ciniki cikin yanci mai inganci cikin gajeren lokaci, wanda hakan ya shaida cewa, bangarorin biyu sun yi imani da juna, kuma batun ya dace bukatun kamfanoni, da bangarorin kasashen biyu. Kuma hakan zai samar da kuzari ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Har ila yau, Switzerland ta tsaya tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, tare da fatan kara yin muamala, da hadin gwiwa tare da kasar Sin, don sa kaimi ga inganta hadin gwiwarsu zuwa sabon matsayi.Bayan ganawar, shugabannin kasashen biyu sun kalli, da daddale takardar kyautata yarjejeniyar ciniki cikin yanci a tsakanin Sin da Switzerland, da kuma takardun hadin gwiwa da dama dake shafar fannonin nazarin kimiyya da fasaha, da samar da aikin yi, da kafofin watsa labaru da sauransu. (Zainab Zhang)














