Szymon Marciniak, alkalin wasan da ya jagoranci wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar, ya amince cewa ya yi kuskure a wasan da aka yi tsakanin Argentina da Faransa.
Marciniak shi ne alkalin wasan farko daga Poland da ya sa ido kan wasan da ya fi kowanne girma da hatsari a kwallon kafa a duniya a ranar Lahadin da ta gabata.
Daga cikin manyan abubuwan da Marciniak ya yi sun hada da bayar da bugun fanareti har sau uku sannan kuma ya bawa dan wasan Faransa Marcus Thuram katin gargadi ba tare da neman shawarar VAR ba bayan shi aka gwabje a cikin zagayen da ake buga fanareti.
Sai dai alkalin wasan mai shekaru 41 ya amince da cewa “kuskure ne”
“Tabbas, akwai kurakurai a wannan wasan na karshe,” kamar yadda Jaridar Vanguard ta nakalto daga kamfanin Sport.PL yayin tattaunawarta da alkalin wasan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp