Daga Abdulrazak Yahuza Jere,
Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta gabatar da rahoton ayyukanta na shekarar 2020, a wani bangare na matakin da hukumar ta dauka a karkashin shugabancin CGI Muhammad Babandede na tattara rahoton ayyukanta a duk shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya kaddamar da gabatar da rahoton a ranar Talatar da ta gabata a shalkwatar hukumar da ke Abuja.
Ministan wanda babban sakataren ma’aikatar, Dakta Shuaibu Belgore ya wakilta, ya yi bayanin cewa rahoton ya nuna cewa NIS ta yi kwazo a shekarar 2020 wanda hakan ya fayyace irin dukufar da NIS ta yi a kan aiwatar da ayyukanta bisa jagorancin ma’aikatar cikin gida.
Da yake yaba wa shugaban hukumar ta NIS, CGI Muhammad Babandede, wakilin ministan ya yi kira ga sauran hukumomin gwamnati su yi koyi da NIS wajen tattara bayanan ayyukansu a duk shekara.
A jawabinsa, CGI Babandede ya bayyana cewa duk da irin dimbin kalubalen da aka fuskanta a 2020 saboda cutar Korona, NIS ta yi tsayuwar daka domin ganin ba ta sare ba a kan ayyukanta da kuma ci gaba da gudanar da sauye-sauye masu ma’ana da ta tasa a gaba.
Babandede ya karfafa gwiwar ‘Yan Nijeriya su yi amfani da damar da aka samu ta gabatar da rahoton na shekara-shekara domin sanin aikace-aikacen hukumar, inda za a samu cikakken rahoton a shafin hukumar na intanet: www.immigration.gob.ng, kamar yadda sanarwar da hukumar ta fitar ta hannun jami’inta na hulda da jama’a DCI Sunday James ta nunar.