Ramadan: Kara Imani Da Allah Shi Ne Mafita – Imam Abubilat Lokoja

Daga Ahmed Muh’d Danasabe, Lokoja

An yi kira ga Al’ummar musulmi da su kara yin imani da Allah madaukacin sarki domin samun tsira a nan duniya da kuma can lahira.

Babban limamin masallacin Isah Kutepa dake garin Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, Imam Yahya Abubilat ne yayi kiran a wajen rufe Karatu da ya saba gabatarwa kowace shekara a babban masallacin na Isah Kutepa dake garin Lokoja, ranan litinin data gabata.

Imam Abubilat wanda yace karatunsa na Ramadanan bana ya mayar da hankali ne akan Tauhidi, wato imani da Allah( SWT) ya kuma kara da cewa imani da kuma tsoron Allah ne kawai zasu ceto mu daga dukkan halin da muka tsinci kanmu ciki, yana mai kira ga Al’ummar musulmi dasu koma ga Allah tare da neman tuba daga Allah domin samu tsira.

Malamin addinin musuluncin ya kuma tunatar da Al’ummar musulmi da cewa akwai tashin kiyama, wato ranan da kowa zai ga sakamakon abubuwan daya aikata yana raye, yana mai jaddada cewa duk abinda mutum ya aikata, zai ga sakamakonsa, wa’alla alheri ko kishiyanta, wato sharri.

A don haka yayi kira ga Al’ummar musulmi dasu san cewa babu abin bautawa sai Allah( SWT) kadai,kuma shi yake warware dukkan hali ko wata matsala  da mutum ya samu kansa ciki.

Imam Abubilat kazalika yace Azumin watan ramadana ya koyar da Al’ummar musulmi darrusa da dama da suka hada da tsoron Allah da son juna da kyautatawa juna da taimakon gajiyayyu da marasa karfi da imani da Allah, wato mayar da lamari ga Allah( SWT) da dai makamancin haka, sannan ya bukaci musulmi dasu tabbatar darrusan da suka koya cikin watan mai tsarki sun dore tare da yin aiki dasu sau da kafa.

Malamin ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yiwa kasa addu’ar samun dawwamammen zaman lafiya, musamman a wannan lokaci da wasu jihohin Nijeriya ke fama da barazanar tsaro da suka hada da matsalar yan bindiga da garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa da kuma uwa uba ta’addanci.

Ya kuma godewa mai martaba Sarkin Lokoja, Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi Na 111 da kuma Alhaji Abdulrazak Isah Kutepa a bisa tallafi da goyon baya da suke bashi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Har ila yau Imam Abubilat ya godewa sauran malamai da kuma al’ummar musulmi wadanda suke bashi hadin kai a yayin gabatar da karatun na Ramadana.
Al’ummar musulmi da dama ne dai suka halarci rufe karatun, cikinsu har da babban limamin garin Lokoja, Ustaz Muhammed Aminu Sha’aban da Sayyadi Nasirudden Yusuf Abdallah da Mallam Tanko Talle da Mallam Tanko Na Yashi da mai shari’a Etsu Umar da Shaba na kasar Kakanda da kuma Wazirin Lokoja, Alhaji Abdulrahman Babakurun.

Exit mobile version