Ranar 26 ga wata June ne Majalisar Dunkin duniya ta ware domin yin Nazarin Kan Matsalar shaye shayen miyagun Kwayoyi a tsakanin al’umma.
mashawarciya ta musamman Kan Harkokin Lafiya ga Gwamna Ganduje, Shugabar Kwamitin Yaki da shaye-shaye ta Jihar Kano sannan kuma Shugabar Kwamitin Lura da masu cutar kwakwalwa Dr. Fauziyya Buba Idris ce ta bayyana Haka alokacin taron Manema labarai data gudanar a ofishinta.
“Sanin kowa ne yadda Annobar Korana ta haifarwa da Duniya mummunar matsà la da har yanzu kokarin farfadowa ake daga illar da annobar ta yiwa duniya. Wannan ne babban dalilin da yasa dole a yiwa Matsalar shaye shayen Miyagun Kwayoyi kallon tsanaki tare da hada hannu da dukkan masu ruwa da tsaki domin fatattakar wannan matsala da ahalin ke neman zamewa al’umma babban kalubalen.
Dr. Fauziyya Buba Idris ta ci gaba da bayyana cewa wannan Rana Ce da Majalisar duniya ta ware domin yin Nazarin tare da bincika yadda za’a dakile wannan annoba ta shaye shayen Miyagun Kwayoyi da yanzu ke neman Zama wata gagarumar matsà la tsakanin matasa maza da matan wannan lokaci. Tace lamarin na tayarwa da duk wani Mai kishin cigaban al’umma hankali.
Hakazalika Kwararriyar masaniyar matsalolin Mata (Gani) ta bayyana cewa duk matsalolin Da ahalin yanzu Suka addabi Jama’a Ba su Wuce wannan Matsalar ta shaye shaye ba, “Idan aka tsinci Kai a irin wannan matsala daga ita ne ake fadawa sace sace, Matsalar Daba, fashi da makami, Garkuwan da Mutane fyade da sauransu.
Tace domin Kawo karshen wannan matsala a Jihar Kano, Gwamna Dakta Abdullahu Umar Ganduje ya kafa wani kwakkwaran Kwamitin Mai mutanen 11 wadanda suke aiki ba dare ba Rana Wajen zakulo hanyoyin dakile yaduwar wannan mummunar ta’ada. Zuwa yanzu alhamdulillahi ana samu gagarumin ci gaba a aikin da ake na magance wannan matsala.
Taken taron na bana shi ne “Ya Za’ayi a samu hanyar Warware wannan matsala Baki Daya” yin hakan Kuma aiki ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa da ake Bukatar Hana hannu domin dakile wannan annoba. Don Haka sai ta shawarci iyaye dasu Kara kaimi Wajen Lura da wadanda yaransu ke mu’amala dasu domin gudun kitso da kwarkwata.
Saboda kyakkyawan fatan da ake dashi, Gwamnatin Jihar Kano ta kafa Kwamitocin tun daga matakin Kananan Hukumomin har zuwa mazabu, wanda kowa ne magidanci zai iya zuwa domin samun Karin haske akan wannan lamari tare da sanar da hukumomi irin halin da wasu yaran ke ciki.
A karshe Dr. Fauziyya ta jinjinawa kokarin da Gwamnati keyi na dakile wannan annoba, sannan ta godewa iyayen Kasa bisa hadin Kan suke bayarwa aduk lokacin da Bukatar Haka ta taso, musamman batun fadakarwa da Wayar da Kan Jama’a Baki Daya.