Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja
A jiya ne gwamnan jihar Kano, Dr. Abudllahi Umar Ganduje, ya rantsar da sababbin kwamishinonin da zai cigaba da aiki da su, inda ya sauke ko kuma ya kori wasu daga cikin waɗanda ya naɗa a baya tun lokacin da a ka rantsar da shi a 2015.
Cikin waɗanda gwamnan ya naɗa akwai riƙaƙƙun masu adawa da tsohon gwamnan jihar kuma wanda shi Gandujen ya gada a kan kujerar gwamnatin jihar, wato Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Misali a nan shi ne, tsohon kantomar ƙaramar hukumar da Kwankwason ya fito, Madobi, kuma tsohon kwamishinan raya karkara a lokacin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, wato Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso.
Iliyasu Kwankwasu ya yi matuƙar fice wajen sukar lamirin Sanata Kwankwaso tun lokacin da a ke ganin Kwankwason ya hana shi takarar majalisar tarayya a 2003, yayin da ya ke zanginsa na farko a mulkin jihar.
Bugu da ƙari, Gwamna Ganduje ya naɗa Hajiya Aisha Ja’afar sabuwar kwamishinar kasafin kuɗi da tsare-tsare. Shi kuwa Alhaji Ahmad Rabiu ya samu muƙamin ma’aikatar kasuwanci da masana’antu ne.
Masu lura da al’amuran siyasar jihar na ganin cewa, yanayin yadda a ka yi naɗe-naɗen ya na nuna cewa, gwamnan jihar ya na nuna cewa, Ganduje na janyo waɗanda za su iya taya shi rikici da tsohon gwamna Kwankwaso ne a 2019.
Bugu da ƙari, a na ganin cewa, kwamishinon da ya sauke har guda biyar hakan na nuni da yadda ya ke son ragewa Kwankwason ƙarfi a cikin gwamnatinsa.
Tuni dai Ganduje ya sallami kwamishinoni guda biyar waɗanda wasu ke kallo a matsayin dukkansu naɗe-naɗe na Kwankwaso a lokacin da ya ke miƙa ƙa Gandujen ragamar jihar, duk da dai cewa gwamnatin ba ta bayyana dalilinta na sauke su ba, kuma sannan gwamnan ya yi ‘siyasar’ cewa, gwamnatinsa za ta “saka su a wani gurbin” lokacin da ya ke jawabin rantsar da sababbi.
To, amma da dama na kallon jawabin nasa a matsayin ƙoƙarin siyasar kwantar da hankalin magoya baya. Cikin waɗanda ya sallama ɗin akwai tsohon shugaban matasa na rusasshiyar jam’iyyar APC, Rabiu Baƙo da Kabiru Ɗandago da Hamisu Lambu da Zubaida Damakka da kuma Haruna Falali, waɗanda a ke ganin dukkansu sun wataya a gwamnatin Kwankwaso.
A jawabin Ganduje ya nuna wa sababbin kwamishinonin cewa, cancantarsu ce ta sanya a ka naɗa su muƙaman, to amma da yawa na da ayar tambayar ko dai ya na nufin cancantarsu a siyasance ne ta yadda za su iya taimakawa tafiyar siyasar yaƙin neman zaɓen 2019.
A wani bincike da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta gudanar a ɓangaren ’yan Kwakwasiyya ta fahimci cewa, canje-canjen da a ka samu ya ba su haushi, kwatankwacin irin canjin da a ka samu lokacin da Ganduje ya sauke Alhaji Rabiu Bichi daga muƙamin sakataren gwamnatin jihar a ka maye gurbinsa da Alhaji Usman Alhaji, da kuma sauya sunan jami’ar jihar da a ka yi daga Jami’ar North West zuwa Jami’ar Maitama Sule.
Idan har hakan ya zamo gaskiya, to kenan a fili ta ke cewa, Ganduje ya na ƙoƙarin tabbatar da ikonsa a cikin gwamnatinsa ta hanyar kakkaɓe gyauron ’yan gani-kashe-nin Kwankwasiyya a cikinta, duba da cewa, akwai tasirin Kwankwaso a sosai naɗe-naɗen muƙamai a farkon gwamnatin ta APC.
Ba a kan wannan ne a ka fara sa zare tsakanin Kwankwasiyya da Gandujiyya ba, domin ko a kan shugabancin jam’iyyar tasu ta APC a na nan a na ta faman kiki-kaka kan waye halastaccen shugabanta na jihar tsakanin Abbas na ɓangaren Gandujiyya na Doguwa na ɓangaren Kwankwasiyya.
Kowanne ɓangare na iƙirarin cewa, shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar. To, amma da irin wannan sauke-sauke da naɗe-naɗe da gwamnan ke aiwatarwa a jihar, a nan ganin cewa, ya na sharewa kansa hanyar samun cikakken iko a cikin gwamnati da kuma jam’iyya ne, domin nan gaba kaɗan taƙaddamar shugabancin jam’iyyar zai iya zuwa ƙarshe da zarar an gudanar da zaɓen shugabannin jam’iyya.
Naɗe-naɗen muƙamai a matakai daban-daban na iya taimakawa wajen dafe madafun iko a kan masu kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓen jam’iyyar, musamman idan wakilai ne za su kaɗa ƙuri’a, ba gabaɗayan mambobi ’yan jam’iyya ba.
Yanzu dai an zura idanu a ga irin matakin da ɓangaren Kwankwasiyya za su ɗauka na mayar da martani kan yadda ɓangaren Gandujiyya ke ta faman gajiyar da su da kuma ƙare mu su ƙarfi a siyasar jihar. Masu iya magana na cewa, ba a san maci tuwo ba, sai miya ta ƙare!