Rashin ganin shugabannin jam’iyyar APC na Jihar Kano a ziyarar ta’aziyya da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya kai ga iyalin Marigayin Alhaji Aminu Dantata, ya haifar da zazzafar muhawara a cikin jam’iyyar.
Rahotanni sun bayyana cewa yayin da jami’an gwamnatin Jihar Kano da ke cikin jam’iyyar NNPP suka yi tururuwan tarbar mataimakin shugaban kasan, ba a ga duriyar shugabannin jam’iyyar APC na jihar ba a wurin wannan taron da ya gudana a ranar Alhamis.
- Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa
- Majalisar Tarayya Ta Karrama NPA Da Kyautar Gaskiya Da Riƙon Amana Ta 2025
Wannan lamari ya haifar da alamomin tambaya, yayin da wasu suna zargin cewa akwai rashi jituwa a cikin APC bayan saukar Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.
Ganduje ya kasance tsohon gwamnan Jihar Kano, wanda har yanzu ke da tasiri a cikin harkokin siyasar jihar, ya yi murabus daga mukamin shugaban APC a ranar 27 ga Yuni, sakamakon lissafin siyasa da shirye-shiryen da aka yi a cikin jam’iyyar kafin zaben 2027.
Masana harkokin siyasa suna ganin cewa wasu daga cikin shugabannin APC a jihar ba su yi farin ciki da murabus din Ganduje a matsayin shugaban APC na kasa ba, kuma suna ganin cewa Shettima ya taka rawa wajen tilasta wa Ganduje yin murabus.
Rahotanin sun bayyana cewa Shettima ya ziyarci Kano ne don yin ta’aziyyar rasuwar hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu kwanan nan, da kuma jajanta wa mutanen Kano kan wannan rashi.
Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa a irin wadannan manyan taruka a Nijeriya, an saba ganin shugabannin jam’iyya da goyon baya su tarbi manyan jami’ai kamar mataimakin shugaban kasa, amma lamarin ya bambanta yayin ziyarar Shettima, wanda ya haifar da zazzafar muhawara.
Da yake musanta cewa akwai rikice-rikice na cikin gida a jam’iyyar, sakataren APC a Kano, Ibrahim Zakari Sarina, ya shaida cewa rashin halartar shugabannin jam’iyyar a ziyarar ta’aziyya da mataimakin shugaban kasa ya kawo Kano ya faru ne sakamakon rashin sadarwa.
“Mun san cewa ziyarar za ta kasance, amma sadarwa ta zo a makare. Kafin mu shirya, mun riga mun makara. Saboda gwamnatin ta riga ta shirya tun kafin mu isa wurin.
“A gaskiya wannan abu ba ya da alaka da kowanne irin lamari na siyasa. An sanar da mu a makare, har ita kanta gwamnatin jihar a makare aka sanar da ita. Daga baya mun aike da godyarmu ga mataimakin shugaban kasa bisa ziyara, kuma ya fahimci yanayin sosai,” in ji Sarina.
Duk da wannan bayani, an samu rarrabuwan kai a tsakanin ‘yan siyasa a jihar.
Wani jigo a APC a yankin Gwale, Abdullahi Kabiru, ya bayyana cewa ya ji takaicin rashin halartar shugabannin jam’iyyar. “Wannan shi ne mataimakin shugaban kasa na wannan kasa, kuma ba mu kasa shirya tarba a gare shi ba? Wannan ba karamin kuskure ba ne. Ko da an samu rashin kyakkyawan sadarwa, yana nuna cewa akwai rashin hadin kai,” in ji shi.
Ita kuwa wata mai kishin jam’iyya, Amina Sani daga Tarauni, ra’ayinta ya sha bamban. Ta ce, “Na gamsu da bayanin da jam’iyyar ta bayar. Abubuwa suna faruwa a siyasa, musamman lokacin da jadawalin ke canzawa. Amma ina fatan hakan ba zai zama sabani ba. Dole ne mu girmama shugabanninmu da ofisoshinsu ba tare da la’akari da kowanne bambancin siyasa ba.”
Da yake jawabi kan lamarnin, wani masana harkokin siyasa, Dakta Musa Auwal ya bayyana cewa dole ne jam’iyyar ta yi taka-tsantsan. “Ko lamarin ya faru da gangan ko akasin haka, a duk lokacin da aka samu rarrabukan na manyan shugabannin jam’iyya a fili, yana rage karfin jam’iyyar kuma yana karfafa ‘yan adawa.
“APC a Kano tana taka muhimmiyar rawa a siyasan kasar nan, kuma kowanne takaddama da ke tasowa Kano na shugabancin ko na siyasa na iya zama babban lamari da ke daukan tsawon lokaci ana tattaunawa a kai,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp