Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi iyakacin kokarinsa wajen tunkarar kalubalen tsaro da Nijeriya ke fuskanta tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2015 “kuma yana barin kasar nan fiye da yadda ya same ta.”
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a Abuja.
- Wang Wenbin: Ayyukan Masu Rajin Neman ’Yancin Kan Taiwan Barazana Ne Ga Tsaro
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda Da Jikkata Wasu A Legas
A yayin da yake fuskantar kwararan bayanai da ke nuna cewa tsakanin watan Mayun 2015 zuwa Mayu 2022, sama da ‘yan Nijeriya 55,000 ne ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da gungun ‘yan bindiga suka kashe, ya ce shugaban kasar nan ya bar yanayin tsaron kasar fiye da yadda ya same shi a shekarar 2015.
“Alkaluman yana raguwa a cikin shekaru da yawa kuma gaskiya ce ta kafa tarihi. Babu wanda zai iya canza shi,” in ji shi.
Da aka tambaye shi ko lamarin ya inganta, sai ya ce, “kwarai da gaske”.
“A shekarar 2015 mun san inda Nijeriya ta ke. Akalla kananan hukumomi 17 na kasar nan suna karkashin ikon ‘yan tada kayar baya.
“Maganar kula, ina nufin suna zaune a fadar sarki, suna zaune a kujerun shugabannin kananan hukumomi. NYSC ba ta iya horar da masu yi wa kasa hidima a wasu yankuna.
“Yau wannan shi ne ke faruwa? A’a, sarakunan sun koma cikin gidajensu. Shuwagabannin kananan hukumomin sun koma ofisoshinsu. Ana buɗlde wa masu yi wa kasa hidima na NYSC a wadannan jahohin kuma ana tura ma’aikatan zuwa jihohin. Yanzu ana so a ce wannan ba sauyi ba ne? A’a, mu kasance masu gaskiya,” in ji kakakin shugaban.
Ya kuma ce nadin shugabannin ma’aikatun bai shafi daidaita kabilanci da ka’idar tarayya ba, inda ya ce shugaban kasa yana da hurumin zaben wadanda yake ganin za su iya tabbatar da kasar nan.
“Kada ku sanya tsaro ga daidaiton kabilanci, kada ku sanya tsaro ga halin tarayya. Hasali ma, kundin tsarin mulkin da ya bayyana halin tarayya har ma ya bai wa shugaban kasa wasu hukunce-hukuncen da zai iya yi da kansa,” in ji shi.