Rashin Tsaro Na Iya Kawo Cikas Ga Aikin Rajista Idan Ba A Dau Mataki Ba – INEC

Hukumar Zabe

Daga Idris Aliyu Daudawa

Yayin da ake gaba da fara yin rajistar masu kada kuri’a hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta  kara jawo hankali wadanda ya dace su yi wani abu dangane da al’amarin rashin tsaro a sassan Nijeria,wanda  a ganin ta hakan na iya kawo mata cikas  ga al’amarin   fara rajistar masu kada kuri’a (CVR).

Amma kuma duk da hakan hukumar ta tabbatar da cewa lalle za a fara aikin rajistar ne a duk fadin Nijeria, kamar dai kowa ya dade da si wato a ranar 19 ga watan Yulinna wannan shekara, wanda kuma abin zai dauki tsawon shekara daya ana yin aikin.

Kamarcdai wata sanarwa wadda ta samu sa hannun Kwamishinan kasa kuma shugaban wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye, ya bayyana cewar ‘yan Nijeriya 42,211 ne suka yi rajista CVR ta yanar gizo. jiya.

Sai dai kuma yayi bayanin wadandabasu samu damar yin rajistar ba ta yanar gizo, ba wani abiun damuwa bane, domin kuwa za su samu damar yin rajisatar lokacin da aka fara yin rajisata, wadda kuma  za ayi ma duk wanda ya cancanta ayi ma shi.

Ya bayyana cewar shi al’amarin rajisata ta yanar gizo “An fara bude hanyar yin rijista ta yanar gizo ta CVR da karfe 7:00 na safiyar ranar Litinin, 28 ga watan Yuni. da kuma karfe 7:00 na safe a ranar 29 ga watan Yuni, sa’o’i 24 bayan kaddamarwar.

An kuma  kirkiri wata dama data kai 59,331duk dai a tsakanin shi lokacin, inda kuma  mutane 42,211 suka nemi da su samu damar yin rajistar, 27,759 da suka nemi sabon aikin rajistar masu kada kuri’a;  yayin da kuma11, 177  suka nemi da a a sabunta masu wadda suke da ita Ya yin da kuma 1, 669 suka nemi da amaida masu da tasu kuria’r zuwa wani wuri, su kuma  853 suka nemi daa yi masu bayanaikan halin daake ciki, su kuwa 335 sun nemi maye gurbin katunan nasu na zabe na dindindin (PVCs) wadanda suka bace ko kuma lalacewa, yayin da su kuma mutane 418 suka nemi  da a basu katin zaben. da  ba akia ga amsa ba. Dukkan wadannan bayanan da suka shafi abubuwan da suka faru a ranar suka kan kafar sadarwa ta zamani ta hukumar.

“Hukumar za ta samar wa ‘ yan Nijeriya bayanan mako-mako kan ayyukanta a kan kafar sadarwa ta zamani, akan halin da ake ciki dangane da rajistar da ake yi da hanyar kafar sdarwa ta zamani, yana kuma da kyau a sanar da ‘yan Nijeriya cewa za a fara aikin yiwa ‘yan Nijeriya rajista wadda za su je da kansu ayi masu a mazabar da suke kusa da ita, ranar 19 ga watan Yuni na shekarar 2021 da kuma matsayin rajistar ta yanar gizo. , a ofisoshin hukumar na  Jihohi da kuma kananan hukumomi  na kasa baki daya.

Wadanda kuma basu samu damar yi ba ta kafar sadarwa ta zamani, za ayi masu da sauran hanyoyin da  ake yi, babu kuma wani dan Nijeriya wandaza a bari ba ayi masa rajistar ba. Za kuma ayi shekara daya ne ana yin ita rajistar.”

Okoye ya ci gaba da bayani inda yake cewa: “shi ma al’amarin daya shafi yin rajisata ta kafar sadarwa ta zamani, za a ci gaba da yin hakan  ranar 19 ga watan Yulin na wannan shekarar 2021,  a dukkannin cibiyoyin yin rajista 2,673  da ake da su yanzu duk fadin tarayyar Nijeriya .

Wannan kuma abin zai kasance ne kamar yadda aka yi la’akari da al’amarin daya shafi tsaro a kasa. Muna kara ma wadanda suke da damar yin rajistar ta yanar gizo, yayin da kuma wadanda basu ita damar su yi hakuri aza afara yin rajisatar gadan – gadan a Nijeriya a ranar 19 ga watan Yuli.”

Exit mobile version