Ana sa ran za a amince da yarjejeniyar Sir Jim Ratcliffe ta zama mai karamin hannun jari a Manchester United a lokacin hutun wasannin kasa da kasa na watan Nuwamba, watakila a farkon mako mai zuwa.
Ana tsammanin rukunin kamfanonin Ineos na Ratcliffe zai biya kusan Yuro biliyan 1.25 don sayen kashi 25 na hannun jari tun bayan da iyalan Glazer na United suka sanar a ranar 22 ga watan Nuwamba na shekara ta 2022 cewa suna tunanin sayar da kungiyar.
- Dan Majalisar Amurka Ya Yi Wa Takwaransa Mahangurba
- Manyan Kalubalen Da Ke Durkusar Da Kiwon Kifi A Nijeriya
Kamfanin Ineos da dan kasar Katar Sheikh Jassim bin Hamad Al Thani sun taya kungiyar inda suka gabatar da tayin kusan Yuro biliyan 5 amma daga baya Sheikh Jassim ya janye daga tsarin ne a watan da ya gabata, yana mai ikirarin cewa tayinsa na karshe, wanda ake tunanin ya ninka darajar Dalar Amurka biliyan 3.2, sai dai bai gamsar da Glazers ba.
Ratcliffe ya sauya niyyarsa ta farko na sayen hannun jarin kashi 69 mallakan Glazers kuma ya rage shi zuwa “mafi rinjaye” amma sai lokacin da ya sake rage shi, zuwa kashi 25 shi ne tsammanin, yiwuwar kulla yarjejeniyar ta karu.
Ratcliffe, wanda ya ce shi masoyin Manchester United ne na tsawon rayuwarsa, ya yi kokarin sayen kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a bara, lokacin da aka saka kungiyar a kasuwa.