Amma Aure ga wanda Allah ya bashi iko, kuma auren bai tauye masa lokacin Ibada ba, ya tsaya da hakkin auren, to wannan daraja ce, irin wannan darajar ita ce a hakkin Annabinmu (SAW).
Wacce yawan matan ba su shagalantar da shi daga hakkin Ubangijinsa ba, kuma su ma matan ya ba su hakkinsu, kai bari ma, yin auren kara masa yawan ibada ya yi kan ibada. Ya ba da hakkin Allah kuma ya ba da hakkin wadanda Allah ya sa a karkashinsa (Iyalansa) ya tsaya wa hakkokinsu na aure da hakkokinsu na ciyarwa da tufatarwa. Ana cewa, yawan aure yana nuna mutum yana da alheri, in mutum bai da alheri dayar ma ba zai iya tsaya wa hakkokinta na ciyarwa da tufatarwa ba.
- Falalar Ziyarar Kabarin Annabi SAW (2)
- Rayuwar Annabi Muhammadu (SAW) Da Abin Da Ya Ta’allaka Da Aurensa (1)
An ruwaito hadisi, Annabi ((SAW)) ya ce “yin aure ba ya daga cikin bukatun duniya ta” ko da cewa aure bukatuwar duniyar wasu ce. Annabi ((SAW)) ya ce: ”Hubbiba ilaiya min dunyakum: An soyar min a cikin duniyarku.” Annabi (SAW) ya yi nuni da cewa, Allah ne ya soyar mai da wasu abu daga duniyar mu, sabida shi komai na shi na Allah ne, ya yi nuni da Abu gida biyu: Turare da Mata.
Manzon Allah (SAW) yana son su don Allah, sabida shi ya soyar masa da su, wannan sabaninmu cewa, muna soyayyar wadannan abubuwan ne don sha’awar duniyarmu, sabida yana sa mu katange idanuwanmu daga matan wasu, ya sa mu kame daga sha’awarmu.
Turare, Annabi (SAW) ya kasance yana son turare sabida haduwa da Mala’iku, babu abin da Annabi ya ki sama da wari, kullun Annabi (SAW) yana haduwa da Mala’iku, a wani Hadisi da Annabi (SAW) ya fada, ya ce, ko nawa mutum ya siya turare bai yi almubazzaranci ba. Bayan fa’idar turare na cewa, sabida Annabi yana haduwa da Mala’iku shi ya sa yake yawan amfani da turare, yana daga cikin amfanin turare, bayan tsarki da saduwa da Ubangiji, yana kara karfin sha’awar aure.
Amma son Manzon Allah (SAW) na hakika, wanda Allah ya kebanci zatinshi da shi, shi ne ganin ikon Ubangijinsa (Hadarar Allah) su Mata da Turare, soyar masa aka yi, da, ko kallo ba su ishe sa ba. Ya fi Annabi Yahya Ma’arifar da ta hana shi aure amma shi Annabi Muhammad (SAW) Hadarar Allah yake kallo da ganawa da shi.
Sabida haka, Manzon Allah (SAW), ya bambance tsakanin wadannan soyayya da halaye guda biyu, da fadinsa “An sanya hasken idanuna a cikin Sallah” za ka ji a hadisi yana cewa Bilalu, kira mana Sallah mu huta, yayin da wasu suke ganin Sallah wahala amma shi Annabi (SAW) a wurinsa Hutu ce, a cikinta yake samun sanyin idanunsa.
Annabi (SAW) ya yi daidai da Annabi Isah da Yahya wajen karewa daga fitinar sha’awar matan, amma Annabi (SAW) ya dara wa Annabi Isah da Yahya wajen cewa shi (Annabi Muhammad) ya yi auren kuma ya tsaya da hakkin Ubangijinsa da hakkin matansa.
Manzon Allah (SAW), shi ne shugaban duk wani namiji, duk wani abu da yake nuna Mazantaka ko namiji ke alfahari da shi, Annabi ya haura kowa: in sadaukanta ce, ya fi kowa, in Kyauta ce, ya fi kowa, in hakuri ne, ya fi kowa, kai ya isa dai a son waye Annabi (SAW), a fadin Ubangiji tabaraka wa ta’ala “Lakad kana lakum rasulullahi uswatun hasanatun liman kana yarjullaha wal yaumal akhir: Lallai ma’aikin Allah ya kasance a cikinku abin koyi…”, Ma’ana duk duniya kowa ya yi koyi da shi.
Yau in aka ce duk mazauna wannan zawiya su yi koyi da mutum daya, lallai kowa ya san an hada wannan mutumin da aiki, ballantana a ce Unguwa, Jiha ko duk Kasar nan kowa ya yi koyi da shi. Amma Annabi Muhammadu (SAW), Allah cewa duk duniya kowa ya yi koyi da shi.
Larabawa, Turawa, Sinawa da mu bakar fata kowa ya yi koyi da shi. Tun da yawan mata, karfin saduwar aure, abu ne da maza ke alfahari da shi, don haka Annabi (SAW) ya fi kowa don ba za a yi wani namiji ya fi Annabi ba.
Yana daga cikin wasan kakacin da aka ruwaito daga Shehu Ibrahim Inyass cewa, akwai wata daga cikin sahabiyarshi, babba ce ta yi aure da yawa tana neman haihuwa ba ta samu ba sai daga baya, in tana lissafin mazajen da ta aura sai ta zagayo carbi, in ta shiga gaida Shehu sai yace mata, yawwa wacce, zo ki lissafa min mazajen da kika aura, nima in lissafa miki matayen da na aura, mu ga ni da ke waye Kudubin.
Akwai ruwayar ba ni Isra’ila, Annabi Sulaiman Matayensa kusan Dubu ne, Annabi Dauda Daruruwa.
Annabi Muhammad (SAW) yana daga cikin wadanda Allah ya ba su karfi da ikon auren Mata ko nawa ne, ba a masa kaidi ba, kuma kowacce ce ta zo ta ce ya Rasulallahi na ba ka kaina, ya amsa, Allah Ya bashi. An ruwaito Sayyada A’isha tana cewa, Ya Rasulullahi ni dai na ga duk abin da kake so sai Allah ya ba ka, amma yanzu a ce kawai da mace ta ce ta ba ka kanta sai ka amsa, ai lalacin matan ya yi yawa.
Sabida wannan karfi da Allah ya bashi, ya halasta masa adadi na ‘ya’ya mata ya aure su shi kadai ban da sauran Mu’uminai. Sabida haka, duk zuriyar Annabi (SAW) su ma Allah ya ba su wannan gadon karfin.
Haka kuma duk wani magajin Annabi (SAW) shi ma Allah ya bashi wannan karfin, Duwatsu sun kasa daukar nauyin Alkur’ani amma zuciyar Annabi ta dauka, sai magadansa Mahaddata, su ma za ka same su da irin wannan karfin na sha’awar aure.
Wata rana Annabi (SAW) ya ba wa Sahabinsa, Zubairu bin Awwami jinin da aka yi masa kaho ya je ya zubar inda babu wanda zai gani, sai zubairu ya shanye jinin, bayan dawowarsa, Annabi (SAW) ya ganshi ya ce ina ka zubar? Zubairu ya bayyana cewa ya zuba a cikinshi, Sai (SAW) ya ce masa “wailul laka minan nasi, wa wailul linnasi minka: ka shiga Uku daga Mutane, su ma mutane sun shiga Uku da kai” Ma’ana yanzun duk makiyina in ya gan ka, kanka zai yi sannan kai kuma duk karfina kanka zai yi, sadaukantakata da damkata, kanka za ta yi.
A kowacce al’ada, mazaje, alfahari suke da auratayya da mazakantaka wajen iyali, sabida haka, wannan abun yabo ne ba zargi ba.
An ruwaito Hadisi daga dan dakin Annabi (SAW), Anas dan Malik, cewa shi manzon Allah (SAW) in ji Anas Ya kasance yana kewaya dakunan matansa a wani lokaci na dare, amma waninsa ba a yarda ba, dole a bai wa ‘ya kwananta. Matan Annabi a wannan lokacin su goma sha daya ne (11) amma mu karshen matan mu hudu (4), duk da cewa, akwai abubuwan da suke kan (SAW) wanda ya zama dole a kansa mu kuma sabanin hakan, kamar kwana ana Sallah, dole ne a kan (SAW) amma mu ba dole ne ba.
Sahabi Anas, ya ce, mun kasance wata rana muna hira, muna cewa shi (Annabi (SAW)) an bashi karfin namiji 30, ma’ana zai iya saduwa da mace 30 a dare daya. Nasa’i ne ya rahoto wannan Hadisin. An sake ruwaito irinsa daga Abi Ra’fi’in (bawan Annabi ne), an karba daga dawusu (almajirin Abdullahi bin Abbas) shi kuma ya ce, an bai wa Annabi (SAW), karfin namiji 40 cikin saduwa da iyali.
An karbo irin wannan hadisin daga Safwan, Salma (baiwar Annabi ce kila kuma baiwar Safiyyatu ce, ungwazomar sayyada Fatima) ta ce, wata rana Annabi (SAW) a dare daya, ya taba kewaye Matansa Tara a wannan lokaci su Tara ne, amma yana yin wankan tsarki kafin yaje wajen ta gaba.
Malamai sun yi sabani cikin adadin yawan Matan Manzon Allah (SAW), amma dukkansu sun tafi, Matan Manzon Allah (SAW) su 11 ne.
Za mu tashi a kan wannan darasi mako mai zuwa in sha Allahu.