Shugaba Bola Tinubu ya ce rayuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta nuna cewa iko ana ba da shi ne domin yi wa jama’a hidima, ba don amfanin kai ba.
Tinubu ya faɗi haka ne a Abuja a wajen ƙaddamar da littafin tarihin Buhari.
- Sin Ta Dauki Matakan Kakkaba Takunkumi Kan Tsohon Shugaban Rukunin Tsaron Kasar Japan
- An Rufe Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Masu Bukata Ta Musamman Ta Kasar Sin Karo Na 12 Da Gasar Olympics Ajin Rukunin Karo Na 9
Ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai gaskiya, ladabi da sauƙin rayuwa, wanda yake ɗauki aikin gwamnati a matsayin amana.
Ya ce gadon da Buhari ya bari ya ta’allaƙa ne kan gaskiya, tawali’u, tsaro, gina manyan ababen more rayuwa da kuma tallafa wa talakawa.
Tinubu ya kuma tuna dangantakarsu ta siyasa wadda ta kai ga nasarar zaɓen 2015.
Tinubu ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta girmama gadon Buhari ta hanyar aiki da gaskiya, tausayi da jajircewa.
Sauran masu jawabi, ciki har da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, marubucin littafin Dokta Charles Omole, da ‘yar Buhari, Hadiza Nana Buhari, sun yaba wa Buhari bisa ladabi, gaskiya da hidimarsa ga Nijeriya.
Taron ya samu halartar manyan shugabanni, sarakunan gargajiya da manyan jami’an tsaro daga sassa daban-daban na Nijeriya da ƙasashen waje.














