Kwanan baya, kamfanin dillancin labarai na Reuters ta ba da labarin cewa, bankin duniya ya ba da takaitaccen rahoto kan tattalin arzikin kasar Sin a ran 23 ga wata, inda ya yi hasashen cewa, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai ragu zuwa kashi 2% a bana, inda a shekarar 2021 zai koma kashi 7.9% sakamakon karin kwarin gwiwar masu sayayya da kamfanoni. Ban da wannan kuma, matakin samar da allurar rigakafi ga al’umma zai kara kwarin gwiwarsu, ta yadda Sin za ta samu bunkasuwa mai karfi. (Amina Xu)
’Yar Xinjiang: Bai Dace Mike Pompeo Ya Tsoma Baki Cikin Harkokin Jihar Xinjiang Ba
Tsohon ministan harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya taba...