Rikicin APC A Kano: Bangaren Shekarau Ya Yi Nasara A Kotu

Daga Sulaiman Ibrahim,

Wata babbar kotu a Abuja ta soke babban taron bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje na jam’iyyar APC.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Hamza Muazu ya amince da babban taron da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau ya jagoranta.

Yanzu haka dai ana takun saka tsakanin Ganduje da Shekarau dangane da jagorantar Jam’iyyar APC a jihar.

Alkalin ya yanke hukuncin cewa taron da ya Kawo mambobi 17,908 yana da inganci.

Alkalin ya kuma bayar da umarnin hana bangaren APC nada sabon shugaban Jam’iyyar.

Bangaren Shekarau ya zabi Alhaji Haruna Ahmadu Danzago a matsayin shugaban jam’iyyar yayin da ‘yan majalisar taron Ganduje suka zabi Alhaji Abdullahi Abbas a daidai lokacin da aka gudanar da taron a ranar 16 ga watan Oktoba.

Kwamitin daukaka kara na kasa da jam’iyyar APC ta kafa ya amince da Abbas a matsayin sahihin shugaban jam’iyyar a jihar.

Sai dai Danzago ya yi watsi da matsayin kwamitin da Dokta Tony Macfoy ke jagoranta, inda ya ce, “Har yanzu hedkwatar jam’iyyar APC ta kasa ba ta amince da kowa ba, amma za ta yi hakan ne a ranar da za ta ba da takaddun shaida ga zababbun shugabannin APC na gaskiya.

Exit mobile version