Connect with us

LABARAI

Rikicin Filato Ta Ci Rayuwar Manajan NCC

Published

on

A cikin wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon rikicin da ya barke a jihar Filato, Zayyanu Shalla wanda babban Manaja ne a hukumar sadarwa ta kasar Nijeriya wato Nigerian Communications Commission (NCC) yana daga cikin wadanda aka kashe su har lahira a rikicin da ke wakanunwa a yankin Jos ta Kudu da ke jihar Filato.
An kashe Manajan NCC din ne hade da wani abokinsa a ranar Lahadi a yayin da ke kan hanyarsa ta dawowa daga wata ziyarar da ya kai jihar Bauchi.
Kamar yadda makusantansa suka shaida, sun ayyanasa a matsayin mutum mai hakuri da juriya suna masu fatan Allah ya gafarta masa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: