Tawagar Nijeriya ta kammala Gasar Haɗin Kan Musulunci ta 2025 da aka gudanar a Riyadh cikin nasara, inda ta ƙare a matsayi na takwas tare da tattara lambobin yabo 30. A rufewar gasar da akayi a daren Juma’a, Nijeriya ta samu zinare 11, azurfa 12 da tagulla 7, abin da ya zama mafi kyawun sakamakonta tun fara halartar gasar.
Rahotanni sun nuna cewa sabon tsarin da Hukumar Wasanni ta Kasa ta ɗauka na zaɓar gwanaye bisa cancanta ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin an samu wannan gagarumar nasara. Ƴan wasan Nijeriya sun shiga wasanni bakwai ciki har da Taekwondo, da Dambe, da Kokawa, da Wasannin motsa jiki, da Ɗaga Nauyi, Para-Powerlifting da Para-Athletics, kuma a kowane rukuni sun samu aƙalla lambar yabo.
- Riyadh 2025: ‘Yan Nijeriya Sun Lashe Zinare A Gudun Zari-Ruga Na Mata
- Sabon Kamfanin Jiragen Sama Na Riyadh Zai Sayi Jiragen Sama Fiye Da 400
Ɓangaren daga nauyi ya fi ɗaukar hankali, inda ya ba wa Nijeriya lambobin zinare 6, da azurfa 4 da tagulla 3. Wasannin motsa jiki sun biyo baya da zinare 2, da azurfa 4 da tagulla 3, sai Kokawa da ta samu zinare 2 da azurfa 2. Para-Powerlifting ta ƙare da zinare guda, yayin da Dambe da Para-Athletics kowannensu ya samu azurfa, Taekwondo kuma ta ɗauko tagulla ɗaya.
Darakta Janar na NSC, Hon. Bukola Olopade, ya bayyana matuƙar jin daɗin sa kan yadda tawagar ta yi aiki tuƙuru tare da kai Nijeriya ga wannan matsayi mai na alfahari, yana mai cewa sakamakon ya nuna cigaba da ingantuwar tsarin wasanni a ƙasar.














