Kasashen Afirka sun dade suna kasancewa masu samar da danyun kayayyaki da ma’adinai, a bisa tsarin samar da kayayyaki na duniya. Sai dai lokaci ya yi da za a kawo sauye-sauye.
A kwanan nan, a birnin Beijing na kasar Sin, ana gudanar da bikin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na duniya a kasar Sin, wato CISCE, a karo na biyu, wanda ya kasance wani muhimmin dandalin da kasar Sin ta kafa don karfafa hadin kan kasashe daban daban, ta fuskar tsare-tsaren masana’antu da na samar da kayayyaki. Kana bikin na da ma’anar musamman ga kasar Sin, da kasashen dake nahiyar Afirka.
- Ɗansanda Ya Gamu Da Ajalinsa Bayan Fasa Tukunyar Miya A Adamawa
- Xi Ya Bukaci A Aiwatar Da Kudurin Kwamitin Sulhun MDD Kan Batun Palastinu
Wani babban dalilin da ya sa kasar Sin kafa bikin CISCE, shi ne domin tinkarar matakan da kasar Amurka da kawayenta na yammacin duniya suka dauka, na kin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda. Wadannan kasashe suna neman rage tasirin kasar Sin a tsare-tsaren masana’antu da na samar da kayayyaki na duniya, ta yadda su da kansu za su sake hawa kujerar jagorancin tattalin arzikin duniya.
Hakika kasashen Afirka sun fahimci nau’in matakan kasar Amurka da na kawayenta sosai, saboda matakai ne na mai da wani saniyar ware, wadanda suka yi kama da matakan da ‘yan mulki mallaka suka dauka a nahiyar Afirka, kamarsu nuna bambancin launin fata, da tilasta wa nahiyar Afirka kasancewa a matsayin mai samar da danyun kayayyaki, da zama babbar kasuwar da ake sayar da kayayyakin masana’antu. A ganin Amurka da kawayenta, ta hanyar hana sauran kasashe tasowa, za su iya kare fifikonsu har abada. Amma dai kamar yadda aka kawar da manufar bambancin launin fata, duk wata manufar da aka tsara, in dai ba ta da adalci, to, tabbas ne za a kawo karshenta a wata rana.
Ko da yake tun daga lokacin mulkin mallaka, an dade ana amfani da tsohon tsarin tattalin arziki wajen danne kasashen Afirka, amma yanzu an fara samun sauyawar yanayi. Bisa wani rahoton da taron ciniki da batun ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya, wato UNCTAD a takaice, ya gabatar, an ce don neman tinkarar matakan kin dunkulewar tattalin arzikin duniya, wasu sabbin masana’antu, irinsu na hada motoci, da kayayyakin latironi, da makamashin ake iya sabuntawa, da magunguna, da kayayyakin aikin jinya, da dai sauransu, suna kokarin raba bangarori masu samar musu da kayayyaki a wurare daban-daban, don magance yiwuwar katsewar hanyar samun kayan da ake bukata. Wannan yanayi, a cewar UNCTAD, na samar da damammaki ga kasashen Afirka, don su taka rawar gani a tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya.
An ce, kasashen Afirka za su iya amfani da fifikonsu na samun dimbin al’umma, da ma’adinai masu muhimmanci, wajen zama kasashen dake samar da sassan kayayyakin da ake bukata a wasu sabbin sana’o’i. Sai dai kafin su iya cimma wannan buri, ya kamata kasashen Afirka su inganta kayayyakinsu na more rayuwa, da horar da ma’aikata, da neman jari da fasahohin da suke bukata. Kana a wadannan fannoni, kasar Sin ta dade tana hadin gwiwa da kasashen Afirka, cikin wani yanayi mai gamsarwa.
Hakika duk wani tsohon tsari, idan aka ga an kawo karshensa a wata rana, tabbas domin yana haifar da rashin jin dadi a zukatan mutanen duniya ne. A nan za mu iya ba da misalin tashar jiragen ruwa ta Chankay ta kasar Peru, wadda aka gina da dalar Amurka biliyan 3.5, a hadin gwiwar kasashen Peru da Sin, tare da burin inganta aikin jigilar kayayyaki cikin tekun Fasifik. Bayan da aka kaddamar da tashar a kwanan baya, shugabannin kasashen Latin Amurka da dama sun bayyana farin cikinsu da kakkyawan fatan da aka sanya a aikin. Amma a nata bangare, gwamnatin Trump mai jiran gado ta kasar Amurka ta yi gargadin cewa, za ta karbi harajin kwastam da ya kai kaso 60%, kan dukkan kayayyakin da aka kai su kasar Amurka da aka bi ta tashar Chancay da su. Dalilin da ya sa take son daukar matakin kawai shi ne, Amurka ta ce, nasarar da aka samu a tashar Chancay za ta iya karfafa gwiwar sauran kasashen dake Latin Amurka su karfafa zumuntar dake tsakaninsu da kasar Sin.
Ta wannan misali za mu iya ganin yadda kasar Sin take kokarin hadin gwiwa da sauran kasashe, da tabbatar da moriyar juna, yayin da kasar Amurka ke neman saka takunkumi da yanke danyen hukunci a kan kasashe da dama, don kare moriyar kanta. Wannan bambanci a sarari ya nuna, shin wane bangare ne yake da adalci. (Bello Wang)