Hukumar Jin DaÉ—in Alhazai Ta Jihar Gombe ta fitar da kashi na uku na jerin sunayen maniyyata 554 a shirye-shiryen tashin su zuwa Madina yau.Â
Jami’in yaɗa labarai na hukumar Muhammad D Muhammad, ya shaidawa LEADERSHIP Hausa cewa, fitar da jerin sunayen biyo bayan nasarar jigilar rukuni na biyu na maniyyatan jihar 560 ne jiya Alhamis zuwa ƙasa mai tsarki.
- Hajjin Bana: Adadin Alhazan Nijeriya A Saudiyya A Yanzun Ya kai 24,324Â
- NAHCON Ta Nemi Alhazai Su Biya Kashi 40 Na Dala 250 Na Jigilarsu
Jihar ta yi sawun farko na maniyyata 560 ne a ranar Laraba, waɗanda suka haɗa da maza 350, mata 205 da jami’ai biyar ta kamfanin jiragen sama na Max Air.
Yayin jawabinsa na bankwana ga maniyyatan jihar a ranar Talata, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya buÆ™ace su da su kasance jakadu nagari ga jihar da Nijeriya, tare da yi wa Gombe da Æ™asar addu’o’i don samun É—aukin Allah game da matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da ake ciki.
Jihar Gombe dai tana da adadin maniyyata 2556 da za su sauƙe farali a aikin Hajjin na bana.