Connect with us

LABARAI

Rundunar ’Yan Sandan Ta Bada Tallafin Naira Miliyan 11 Ga Iyalan Jami’anta Da Suka Rasa Rayukansu A Kebbi

Published

on

A jiya rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta bayar da tallafin Naira Miliyan goma sha daya ga Iyalan jami’an ta gudu goma da suka rasa rayukansu a fagen a jihar Kebbi a jiya a Birnin-Kebbi.
An dai gudanar da bukin bayar da tallafin ne a hedkwatar rundunar ‘yan sandan da ke a Birnin-Kebbi a jiya. Haka kuma iyalan jami’an da suka ci gajiyar tallafin sune na wadanda suka rasa rayuwar su tun daga shekara ta 2015 zuwa ta 2017 a jihar ta Kebbi.
Hakazalika iyalan marigayan da suka amfana daga tallafin kudaden sun hada da insifeto Dauda Muhammad, Insifeto Bahago Gosa, sajan Lahadi Isah da kuma sajan Mathew Mutuwa.
Sauran sun hada da ASP Yakubu Yahaya, Insifeto Yakubu Usman, Insifeto Suleiman Umar, sajan Habila Lebi, CPL Ahmed Tijani da kuma CPL Shehu Aliyu.
Yayin da yake gabatar da tallafin kudaden ga iyalan marigayar, Kwamishinan rundunar ‘yan sandan ta jihar Kebbi CP Kabiru M. Ibrahim ya bayyana cewa “wannan tallafin an bayar da shine domin inganta zaman rayuwar iyalan marigayar da kuma kyakyawar kulawa ga yaran da marigayan suka bari”.
Haka kuma Kwamishinan yayi kira ga iyalan marigayan da suka amfana da wannan tallafin da su tabbatar da sun yi amfani da tallafin ta yada ya kamata. Har ila yau ya ci gaba da cewa shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya, watau insifeto janar Ibrahim Idris, shine ya bada umurnin bayar da tallafi ga iyalan marigayan jami’an ‘yan sanda a kasar Najeriya domin bada muhimmiyar kulawa ga iyalan marigayan da kuma tabbatar da cewa yaransu sun yi karatu maizurfi domin su iya dogaro da kansu.
Bugu da kari ya ce tsarin bayar da tallafin tsari ne wanda za a ci gaba da bayar wa ga tun iyalan aka mutu aka barsu. Saboda haka rundunar za ta ci gaba da tallafawa domin ganin cewa iyalan marigayan jami’an ‘yan sanda basu shiga wani hali ba.
Daga karshe kwamishinan ya godewa shugaban rundunar na kasa kan bayar da umurnin tallafawa iyalan marigayan jami’an rundunar da kuma iyalan marigayan kan hakurin rashin da suka yi na mazajen su.
Advertisement

labarai