Connect with us

LABARAI

Ruwan Rafi Ya Cinye Yara Biyu A Jigawa

Published

on

Ruwa ya yi sanadiyyar mutuwar yara 2 a yayin da suke wanka a wani rafi a kauyen Gantsa dake karamar hukumar Buji ta jihar jigawa.
Jami’in watsa labaran hukumar Cibil Defense NSCDC ta jihar Jigawa, Adamu Shehu, ya tabbatar wad a maneman labarai faruwar lamari a ranar Juma’a a garin Dutse.
Mista Shehu, ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yamman ranar Alhamis.
Jami’in watsa labaran ya ce, sunayen mamatan sun hada da Yusuf Adamu, dan sgekara 6, da Umar Ibrahim, dan shekara 4, an kuma tabbatar da mutuwar su ne bayan da aka kaisu asibiti inda likita ya bayana cewa, lallai sun rigamu gidan gaskiya.
Daga nan ya shawarci iyaye a fadin jihar dasu kula da zirga zirgan yaransu don kaucewa irin wannan mugun lamarin.
An ruwaito cewa, a ranar 7 ga watan Disamba na shekarar 2017, wasu ‘yan mata 4 suna mutu a yayin da sukre wanka a rafin Sakwaya dake karamar hukumar Dutse ta jihar.
Haka kuma a ranar 8 ga watan Yuli na shekarar 2017, rundunar ‘yan sandan jihar ta hannun jami’in watsa labaranta Abdu Jinjiri ta sanar da cewa, fiye da mutum 11 suka mutu sanadiyyar fadawa a rafi a fadin jihar a cikin wata daya tak.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: