Ƙasar Rwanda ta musanta cewa ba ita ke haddasa sabbin rikice-rikicen da ya kunno kai a Kibu ta Kudu da ke DR Congo.
Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da ma’aikatar harkokin wajen Rwanda ta fitar.
Rwanda ta kuma zargi rundunar DRC da ta Burundi, tare da mayakan FDLR da Wazalendo da wasu ‘yan kasashen waje da kai hare-hare da jiragen yaki marasa matuka kan kauyuka kusa da kan iyakar Rwanda.
- Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP
- Sin Ta Yi Kira Da A Gaggauta Tsagaita Bude Wuta A Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo
Rwanda ta ce hakan ya tilasta wa sama da ‘yan Congo 1,000 tserewa zuwa kasar, inda aka basu masauki a Bugarama.
Haka kuma, Rwanda ta ce Burundi ta tura sojoji 20,000 a Kibu ta Kudu domin yi wa al’ummar Banyamulenge a Minembwe kawanya.
Rwanda ta yi gargadi cewa irin wadannan matakai na kawo barazana ga zaman lafiya a yankin, tana mai kira a koma ga yarjejeniyar da Amurka ke mara wa baya da kuma kammala sauran sashe na yarjejeniyar Doha tsakanin DRC da M23/AFC.














