ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP

by Leadership Hausa
7 months ago

Siyasa a Nijeriya ta dauki wani zazzafar muhawara a wannan lokaci. A kusan kowane lokaci, manyan jam’iyyun siyasa a kasar sun sha ganin mutane suna yin murabus da barin jam’iyya kai tsaye da sauya sheka da kokarin rajistar sabbin jam’iyyun siyasa da sauran dabaru na siyasa.

Wannan ya kai ga yadda mutane ba za su iya cewa a fili inda shugabanninsu suke ba, kuma kusan ba za su iya bambanta jam’iyyun siyasa ba saboda yawan sauya sheka na shugabannin siyasa.

  • Ƴan Majalisar Dokokin Jihar Ribas 16 Sun Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC
  • Tsohon Gwamnan Kaduna, El-Rufai, Ya Fice Daga SDP, Ya Koma ADC

Duk da takun saka, jam’iyyar APC ce ta samu riba mafi yawa a cikin rikicin PDP, sai jam’iyyar ADC ita ma ta amfana da rikicin.

ADVERTISEMENT

Jam’iyyar PDP a gefe guda tana cikin mawuyacin hali, inda take fuskantar mafi munin rarrabuwar kawuna a tsakanin mambobinta.

Ta rasa tsohon mataimakin shugaban kasa da abokin takarar shugaban kasa na zaben 2023, da yawa daga tsoffin gwamnonin da ke kan kujeru, da kuma tsofaffi da mambobin majalisar kasa da ke kan kujeru.

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

PDP wanda ke da gwamnonin 11 bayan zaben 2023, yanzu tana da biyar kawai tare da karin wasu suna nuna suna son barin jam’iyyar.

Yawancin gwamnonin da suka sauya sheka a cikin wannan lokaci sun koma APC, yayin da jam’iyyar Accord ta samu guda daya.

Gwamnonin da suka bar PDP zuwa APC su ne Umoh Eno na Akwa Ibom da Sheriff Oborebwori na Delta da Douye Diri na Bayelsa da Peter Mbah na Jihar inugu. Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya dade yana son barin PDP kuma yanzu yana jiran lokaci mai ya yi ne ya shiga APC.

Akwai fargaba cewa gwamnonin Caleb Muftwang na Jihar Filato da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ma na iya canza sheka. Gwamnonin PDP kadai da suka bayyana a fili cewa za su tsaya cikin jam’iyyar don gyara al’amuran gida su ne gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad da abokin aikinsa na Jihar Oyo, Seyi Makinde, yayin da Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa ya bayyana tamkar yana son sauya sheka.

Rikicin PDP y afara kuno kai ne tun bayan zabukan 2023, baya ga gwamnoni, jam’iyyar ta rasa karin ‘yan majalisa, ciki har da manyan mambobin majalisar tarayya zuwa APC.

Daga cikin ‘yan majalisar tarayya da suka bar tsohuwarsu zuwa APC akwai Sanata Agom Jarigbe daga Jihar Kuros Ribas da Sunday Marshal Katung daga Kaduna.

Tun daga shekarar 2023 har zuwa yanzu, jam’iyyun adawa a majalisar wakilai sun rasa akalla mambobi 66 zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP wadda ta rasa ‘yan majalisu 44, sai LP 14, NNPP 6, ADC 1 da YPP 1.

A lokacin da aka kaddamar da majalisar a watan Yuni 2023, tsarin majalisar wakilai ya kasance APC tana da kujeru 178, PDP 115, LP 35, NNPP 19, APGA 5, SDP 2, YPP 2 da ADC 2.

Bayan guguwar sauya sheka, yawan ‘yan majalisar yanzu sun kasance kamar haka: APC 246, PDP 71, LP 21, NNPP 13, APGA 5, SDP 2, ADC 1 da YPP 1.

A ranar Juma’a da ta gabata, mambobi 16 na majalisar dokokin Jihar Ribas karkashin jagorancin shugaban majalisan, Martin Amaewhule, sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Lokacin da aka kaddamar da majalisar dokoki ta kasa ta 10 a ranar 13 ga Yunin 2023, jam’iyyar APC ta rike kujeru 59 a majalisar dattawa.

Amma jam’iyyar ta kara tumbatsa zuwa samu sanatoci 76, ta wuce kashi biyu bisa uku na samun rinjaye, bayan samun sauya sheka da ‘yan majalisar dattawan suka shiga cikinta.

Lokacin da aka amince da ADC a matsayin jam’iyyar hadaka ta tsofaffin shugabannin PDP, jam’iyyar ta sami sabon rayuwa tare da shigowar manyan mambobin PDP da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark da tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola da wasu.

Yawan wadanda ke barin PDP suna shiga APC ne, yayin da kadan daga ciki suke shiga ADC.

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufai ya sauya sheka daga APC zuwa SDP, sannan daga baya ya shiga ADC.

PDP ita ce kawai babbar jam’iyya da ba ta amfana daga guguwar sauyin sheka ba, amma tana ci gaba da rasa babban adadin mambobinta.

Wani masanin siyasa kuma farfesa a fannin kimiyyar siyasa, Gbade Ojo, wanda ya yi magana da wakilinmu kan wannan batu, ya lura cewa rushewar jam’iyyun adawa yana da babban tasiri wajen yawan tserewar mambobi, yana mai cewa hakan ya kara rage gwarin gwiwar al’ummar Nijeriya.

“Idan ka kalli majalisa, APC yanzu tana da gagarumi rinjaye a duka majalisar wakilai da majalisar dattawa. Ayyukan sa ido nasu suna da rauni sosai saboda shugaban kasa ya nada jami’an da su ne za su je su gudanar da ayyukan sa ido a kansu. Amma yawancinsu yanzu suna cikin jam’iyyar gwamnati,” in ji shi.

Sau da dama PDP ta yi kokari dawo da martabar jam’iyyar. Ta gudanar da babban taro a matakin gundumomi da karamar hukumomi da jihohi da dama kuma kasa baki daya, inda mambobi suka zabi sabon shugaban jam’iyyar na kasa.

Amma lamarin ya ci tura, inda magoya bayan ministan Abuja, Nyesom Wike suka kalubalantar babban taron.

Wasu na cewa ko da an gudanar da babban taron zaben, jam’iyyar ta kasa haifar da irin amincewar da zai sa mambobinta su ci gaba da kasancewa wuri guda.

Duk da yake akwai alamun da ke cewa ko wadanda suka saura na iya barin jam’iyyar a kowane lokaci.

Masana na cewa ci gaban rikicin a jam’iyyar da shari’o’i da dama na iya sanya ‘yan takararta a 2027 cikin hadari ta fuskar doka, musamman gwamnonin da ke neman wa’adi na biyu su nemi wasu jam’iyyar.

A hankali, ADC tana samun karuwa a matsayin babban jam’iyyar adawa a kasar, tana matsar da PDP zuwa baya, wacce ta rike wannan matsayi tun bayan ta fadi a zaben shugaban kasa a 2015, zuwa matsayi na biyu.

A kwanan nan, jam’iyyar ta ce tana shirin karbar sama da mambobin majalisar ta 10 guda 100 kafin zaben shekarar 2027.

A halin yanzu APC na da yawancin ‘yan majalisa a duka majalisun dokoki kasar nan tare da zargin cewa wasu na shirin shiga jam’iyyar.

Akwai rahotannin da ke cewa a jihohi kamar Benuwai, Kano, Adamawa da Yobe cewa ADC ta kafu kuma za ta bunkasa c

ikin ‘yan watanni kadan masu zuwa.

ADC
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

MASU ALAKA

Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Manyan Labarai

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC
Manyan Labarai

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Borno

July 14, 2026
Next Post

GORON JUMA'A 12/12/2025

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026
Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.