Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da farashin aikin Hajjin 2026, inda aka samu ragin kaso 9.7% cikin ɗari idan aka kwatanta da farashin Hajjin bara 2025.
A cewar sanarwar da shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya fitar ranar Juma’a da daddare, alhazai daga gundumar Maiduguri–Yola (Borno, Yobe, Adamawa da Taraba) za su biya N8,118,333.67, yayin da sauran jihohin Arewa za su biya N8,244,813.67. A gefe guda kuma, alhazai daga jihohin Kudu za su biya N8,561,013.67. Wannan na nufin cewa kowanne mai niyyar tafiya Hajji a bana zai samu ragin kimanin N200,000 ƙasa da farashin 2025.
- EFCC Ta Kama Daraktocin NAHCON 2 Kan Zargin Karkatar Da Kuɗin Hajjin 2025
- Hajji: NAHCON Ta Kammala Jigilar Kashi 77 Na Mahajjatan Nijeriya Zuwa Saudiyya
Farfesa Usman ya ce farashin ya biyo bayan doguwar tattaunawa da shugabannin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki tare da amincewar gwamnatin tarayya. Ya kuma bayyana cewa tawagar NAHCON da ke Saudiyya ta riga ta rattaba hannu da kamfanin Mashareeq Al-Zahabiyya a matsayin mai kula da walwalar ƴan Nijeriya na Hajjin 2026 da kuma kamfanin sufuri na Daleel Al-Ma’aleem.
Shugaban NAHCON ya buƙaci duk masu niyyar tafiya aikin Hajjin 2026 da su kammala biyan kuɗinsu kafin ranar 31 ga Disamba, 2025. Ya ce wannan tsari zai ba da damar shiryawa cikin lokaci, tare da tabbatar da ingantaccen sufuri da wuraren masauki ga dukkan mahajjata daga Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp