Khalid Idris Doya" />

Sabon Gwamnan Bauchi Ya Rantsar Da Manyan Direbobin Gwamnatinsa

Gwamnan Bauchi

A jiya Litinin ne gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala A. Muhammad ya rantsar da Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin jihar, da kuma mataimakin shugaban ma’aikata na gidan gwamnati da ke zai yi aiki a ofishin mataimakin gwamna, hade da kalubalantarsu wajen yin aiki tukuru don kyautata jihar da kaita mataki na gaba.

Bikin shan rantsuwar wacce ta gudana a darin taro na Bankuet Hall da ke gidan gwamnatin jihar, inda ‘yan uwa da abokan arzikin wadanda aka rantsar suka kasance bakin domin shaida amsar rantsuwar tasu.

Wadanda gwamnan ya rantsar sun hada da Alhaj Mohammed Sabi’u Baba a matsayin Sakataren gwamnatin jihar Bauchi (SSG), Alhaji Abubakar Kari a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati (Chief of Staff), a yayin da kuma Alhaji Bashir Ya’u ya zama mataimakin shugaban ma’aikata da zai yi aiki a karkashin ofishin mataimakin gwamna.

Babban Jojin jihar Bauchi, Justice Rabi Talatu Umar ce ta rantsar da su, inda ta samu wakilicin Justice Ahmed Mohammed Kabir Madaki, inda su kuma suka dauki alkawarin gudanar da ofisoshinsu bisa tsarin gudanar da aiki.

Da yake jawabinsa a wajen bikin, gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammad ya ce an nadasu da rantsar da su ne domin su taimaka gwamnatin jihar wajen gudanar da gwamnati cikin ruwan sanyi, yana mai tabbatar da cewar SSG, da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati da mataimakinsa suna daga cikin muhimman kusoshi na tafiyar da gwamnatin jiha, don haka ne ya nemi su da kada su watsa masa kasa a ido.

Ya ce; “Yanzu lokacin zabe ya wuce, yanzu lokaci ne na maida hankali wajen gudanar da kyawawan aiyukan gudanar da gwamnati da tabbatar da yin kyawawan aiyuka domin kaiwa ga cimma alkawuran da muka yi ga wadanda suka zabemu.

“Don kaiwa ga cimma ababen da jama’a ke tsammani daga gwamnati, akwai bukatar nada nagartattu, amintattu kuma gogaggun mutane a kujeru daban-daban,” A cewar shi.

Bala yana mai cewa nadin da yayi ga wadannan mutanen an yi ne bisa dacewarsu da kuma tsantsar biyayyarsu, kana ya nemi su tabbatar da yin aiki tukuru domin ci gabantar da jihar Bauchi.

Da ya ke jawabi a madadin wadanda suka nada, Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Alhaji Muhammad Sabi’u Baba ya gode wa gwamnan jihar a bisa zabinsu da yayi hadi da basu wadannan mukaman, yana mai tabbatar wa gwamnan cewar za su zage damtse wajen yin aiki tukuru domin cimma manufar da aka sanya gaba, “Ina tabbatar maka za mu yi aiki tare domin tabbatar da kai jihar Bauchi zuwa ga babban matsayi,” Inji shi.

Sauran nade-naden da gwamnan ya yi tare da wadanda aka rantsar jiya, sun hada da Alhaji Umaruji Hassan a matsayin babban mai tsare-tsare na gidan gwamnati, da kuma Mukhtari Gidado a matsayin babban mai taimaka wa gwamnan kan hulda da ’yan jarida.

Exit mobile version