A yayin da a halin yanzu kafafen sadarwa na zamani ke bayar da gudummawa wajen ci gaban harkokin kasuwanci a fadin duniya, an samu wata tashar talabijin da ta fara gabatar da wani shiri mai suna ‘Influencer Abe’ wanda yake tattaro bayanai daga masana a kan wasu sabbin hanyoyin kasuwanci a fadin Nijeriya.
A sanarwa da kamfanin da ke gabatar da shirin mai suna ‘The Arkerson Agency’ ya bayyana cewa, an kirkiro da Shirin ne don karfafa matasa masu tasowa yadda za su ci gajiyar hanyoyin kasuwanci a Nijeriya wadanda ba a san da suba a baya.
- An Maido Da Huldar Diplomasyiya Tsakanin Sin Da Nauru, CMG Ta Bude Ofishinta A Nauru
- ‘Yansanda Sun Karyata Jita-jitar Kai Harin Garkuwa Da Mutane A Jami’ar BUK
Dea yake karin harske a kan yadda shirin zai amfani al’umma, mai magana da yawun kamfanin, Uju Obiejesi,ya ce, shirin na ‘Influencer Abe’ zai zama mattarar matasa masu hazaka da kuma suka tsunduma harkokin kasuwanci don su bayyana wa al’umma irin yadda suka samu kansu a cikin harkokin kasuwancin, za su kuma bayyana irin kalubalen da suke fuskanta da kuma irin nasarorin da suka samu, domin hakan ya zama darasi ga matasa masu shirin shiga harkokin kasuwanci a na gaba.
Ta kara da cewa, akwai bangarori da dama na harkokin kasuwanci da al’umma basu mayar da hankali a kai, amma wannan shirin zai haska wa mutane tare da karfafa su don su shiga a dama da su.
Haha kuma shirin zai taimaka wajen wayar da kan al’umma hanyoyin da za su amfana da tallafin da gwamnati ke bayarwa ga masu harkokin manya da kananan masana’antu. ‘Mun lura al’umma da dama sun kasa cin gajiyar tallafin da ke fitowa daga gwamnatin tarayya dana jihohi saboda basu san yadda za su fuskanci lamarin ba.