Sabon shugaban karamar hukumar Lokoja, Hon Muhammed Danasabe a ranan Talata daya gabata ya shaida binkin rantsar da sabbin kansiloli 10 da aka zaba karkashin tutar jam’iyyar APC a zabukan kananan hukumomi da aka gudanar a ranan Asabar 12 ga watan Disambar 2020.
Kansilolin sun sha rantsuwar ne a gaban akawun majalisar karamar hukumar, Mallam Muhammed Alfa.
Bikin wanda aka gudanar a zauren majalisar karamar hukumar ta Lokoja, ya samu halarcin sarakunan gargajiya da mahukuntar karamar hukumar da shugabannin jam’iyyar APC na gundunomi da kuma sauran masu ruwa da tsaki dake karamar hukumar ta Lokoja.
Shugaban karamar hukumar Lokoja, Hon Muhammed Danasabe Danasabe, a jawabinsa ya jinjinawa gwamna Yahaya Bello a bisa gudanar da zabuka masu tsafta, sahihai kuma karbabbu a majalisun kananan hukumomi dake fadin jihar Kogi.
A matsayina na shugaban karamar hukumar mai cikakken iko,ina baku tabbacin cewa shirye nake na gina kyakkyawan dangantaka tsakanina daku.A don haka nake bukatarku da ku kasance tare da jama’arku a kowani lokaci tare da ganin kun rika tunawa da kyawawan manufofin gwamnatin mai girma gwamna Yahaya Bello wadda burinta shine kula da mutane daga kasa. Dole ne ku rika yin koyi da salon gwamnati irin na mai girma gwamna,” in ji Hon Muhammed.
Har ila yau ya yi amfani da wannan biki,inda ya jinjinawa shugabancin jam’iyyar APC a bisa irin gagarumin rawar da suka taka a yayin zabukan.
Daga bisani ya taya sabbin Kansilolin murna, a dai dai lokacin da su ke shirin wakiltar al’ummar mazabunsu daban-daban.
Da ta ke mayar da jawabi a madadin sauran Kansiloli 10 dake karamar hukumar ta Lokoja, kansila mai wakiltar mazabar gundumar Ward A, Hon Bala Blessing Ogwu, ta godewa gwamna Yahaya Bello a bisa samarwa da jama’a daga kasa gwamnatin da su ma za su san ana damawa da su.
Har ila yau ta yabawa shugabannin jam’iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki a bisa jajircewarsu na ganin jam’iyyar ta samu nasara a zabukan.
A don haka nema ta baiwa sabon shugaban karamar hukumar tabbacin samun cikakken hadin kan Kansilolin a dai dai lokacin da zasu kama aiki gadan gadan da zimmar kyautata rayuwar al’ummar mazabarsu dake karamar hukumar ta Lokoja.
Sabbin Kansilolin da suka sha rantsuwar sun hada da Hon Bala Blessing Ogwu, Salisu Suleiman Bala, Adam Rukayyat Lami, Bashir Salihu da kuma Abdulsamad Umar.