Gwamnatin Jihar Sakkwato, ta bayyana damuwarta kan bayyanar wata sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda mai suna LAKURAWAS.
Ana zargin kungiyar da aikata miyagun ayyuka a kananan hukumomi biyar na jihar.
- Kotu Ta Soke Tuhumar Da Ake Yi Wa Yaran Da Aka Kama Yayin Zanga-zangar Yinwa
- Yau Amurkawa Ke Kaɗa Ƙuri’ar Zaɓen Shugaban Ƙasa
Mataimakin gwamnan jihar, Idris Mohammed Gobir, ya bayyana kungiyar na amfani da sunan Addini, kuma tana da makamai, lamarin da ya kara ta’azzara matsalar ‘yan bindiga a jihar.
Gobir, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro suna aiki tare da hukumomin tsaro na tarayya don magance wannan barazanar.
Ya yi wannan bayanin ne yayin da yake karbar baki daga Kwalejin Tsaro ta Ƙasa (NDC) wadanda suka ziyarci jihar domin gudanar da bincike.
Shugaban tawagar NDC, Air Vice Marshal Titus Dauda, ya ce za su mika rahoton bincikensu ga gwamnatin jihar don taimakawa wajen magance matsalolin tsaro.
Ayyukan ‘yan bindiga na ci gaba da wakana a jihar, inda mahara suka kashe mutane da dama tare da raba wasu da muhallansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp