Connect with us

BABBAN BANGO

Sai An Zubar Da Ruwa A Kasa Kafin A Taka Damshi

Published

on

Masu iya magana na cewa, idan ka ga Wane, aka ce ba Banza ba. A yayin da har yanzu wasu sassa na duniya ke fama da annobar COVID-19, a hannu guda kuma, kasar Sin ta samu gagarumar nasara wajen shawo kan wannan annoba. Wannan ne ma ya sa ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani, kan ayyuka da matakan da kasar ta dauka na yaki da cutar COVID-19 a kasar, inda aka yi bayani dalla-dalla game da matakan da kasar ta dauka wajen yaki da cutar COVID-19.

An kasa wadannan matakai zuwa kashi hudu, wato kokarin kasar Sin wajen yaki da cutar COVID-19, da ayyukan hadin gwiwa na magance cutar da bada jinya ga wadanda suka kamu da cutar, da yadda kasar ta hada kai da kasashen duniya da kungoyin kasa da kasa wajen yaki da cutar da kuma kokarin kafa al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama a fannin kiwon lafiya.
Da farko, wasu kasashen yamma sun soki matakan da kasar Sin ta yi amfani da su wajen yakar wannan annoba, amma daga bisani, wadannan salon da kasar Sin ta yi amfani da su wajen tinkarar annobar, sun zama tamkar abin koyi ga sauran kasashen duniya, wanda ya kunshi jami’ai da hukumomin gwamnatin kasar, hukumomi masu zaman kansu gami da daidaikun jama’a, duk sun hada karfi da karfe wajen tinkarar annobar.
Wani abin farin ciki da karfafa gwiwa shi ne, tun bayan barkewar cutar ta COVID-19 a kasar, babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar, kana shugaban kasar Xi Jinping, shi da kansa, ya jagoranci aikin dakile cutar inda ya jaddada bukatar ba da muhimmanci ga rayuka da lafiyar jama’a. Wadannan kalamai na shugaban kasar Sin game da ba da muhimmiyar kulawa ga lafiyar jama’a, ya yi gagarumin tasiri a yaki da annobar, domin matakin ya baiwa al’ummar kasar kwarin gwiwa, wajen bada cikakken hadin kai da kuma shiga a dama da su, kamar yadda masu iya magana ke cewa, Hannu Daya ba shi Daukar Jinka, wannan ya sa al’ummar Sinawa kara sadaukar da kai da ba da hadin kai ta yadda za a gudu tare a tsira tare.
Irin wadannan gudummawa na kishin kasa da kowane Basine ya bayar gwargwadon hali domin ganin an kai ga nasara, ya taimaka wajen fitar da Jaki daga Duma.
Sanin kowa ne cewa, a halin yanzu, dukkan al’ummar duniya na fuskantar kalubalen kiwon lafiya mafi tsanani da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan yakin duniya na biyu.
Duniya ta shaida cewa, kasar Sin ta yi namijin kokarin yaki da cutar, da tabbatar da tsaron rayuka da lafiyar jama’a. Haka kuma, Sin ta dauki matakai a dukkan fannoni wajen magance cutar, da kula da jinyar dukkan wadanda suka kamu da cutar a kasar, har ma ta mayar da hankali wajen taimakon sauran kasashen duniya da fasahohi da dabaru da masana da na kayayyakin yaki da wannan annoba dake neman gagaran kwandila.
Takardar ta kara da nuna cewa, hadin gwiwar kasashen duniya, shi ne babban makami wajen yaki da cutar. Kuma tun lokacin da cutar ta bulla a Wuhan dake kasar ta Sin, mahukunta suka rika sanar da kasashen duniya dukkan muhimman bayanan da ake bukata ba tare da boye komai ba da kuma mika dukkan abubuwan dake shafar cutar ga hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO da kuma kasashen da abin ya shafa, tare da samar da gudummawa da amfani da fasahohi wajen yaki da cutar ga duniya baki daya. Tun da gaskiya ta tabbata, ya kamata ’yan siyasar Amurka su daina babatun da suke yi na neman shafawa kasar Sin kashin kaji kan wannan annoba, maimakon haka, su mayar da hankali wajen taimakawa jama’arsu fita daga radadin wannan annoba.
Alkaluma na nuna cewa, ya zuwa karshen watan Mayu, kasar Sin ta riga ta samar da gudummawa ga kasashen duniya kimanin 150 da hukumomin kasa da kasa 4, da tura tawagogin masanan kiwon lafiya ga kasashe 24 da suka fi bukata, da gudanar da tarukan magance cutar ta kafar bidiyo ga kasashen duniya fiye da 170, da kuma kara samar da kayayyakin kiwon lafiya da na’urori ga duniya baki daya. Jama’a daga bangarori daban daban na kasa da kasa sun yi nuni da cewa, Sin ta martaba tunanin kafa al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama, da daukar alhakinta, kuma kasashen duniya sun yaba mata matuka a wannan fanni.
Baya ga matakan shawo kan wannan annoba da gudummawar kayayyaki da ma’aikatan kiwon lafiya da kasar Sin ta rika turawa sauran kasashe na duniya, mahukuntan kasar Sin sun kuma tsara matakan dawo wa bakin aiki, a bangaren kamfanoni, da masana’antu, da makarantu da ofisoshi da sauransu, ba tare da cutar ta sake yaduwa ba.
Al’ummar duniya na iya warware manyan matsalolin cututtuka ta hanyar yin hadin gwiwa da yin kokari tare. Yayin da ake tinkarar cutar COVID-19, jama’ar kasa da kasa sun yi kokari tare da yin hadin gwiwa don yaki da cutar tare. Hausawa na cewa, har yanzu ba a rabu da Bukar ba, ma’ana har yanzu, cutar COVID-19 ba ta kare ba, don haka, akwai bukatar kasashen duniya su ci gaba da yin kokari da daukar matakai don magance cutar.
Masana sun bayyana cewa, ya kamata kasashen duniya su ci gaba da baiwa hukumar WHO goyon bayan da ya dace, ta yadda za ta ci gaba da jagorantar ayyukan magance cutar, da ma sauran cututtukan dake damun daukacin bil-Adama a duniya, masu azancin magana na cewa, ko a gidan Giya akwai babba, maimakon neman yin hannun riga da hukumar, kamar matakin Amurka na ficewa daga zama mambar hukumar, ya dace a kara nuna goyon baya ga kasashen Afirka, da kyautata tsarin kiwon lafiya na duniya, da kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa don inganta karfin kasashen duniya wajen yaki da cutar.
Takardar bayani game da matakan da kasar Sin ta dauka wajen yaki da cutar COVID-19 ta shaida kokarin kasar wajen inganta tsarin kiwon lafiyar dan Adam, wanda za a iya tabbatar da tsaron rayuka da lafiyar daukacin bil-Adam. Lafiyar dan Adam shi ne tushen samun ci gaban zamantakewar al’ummar duniya.
Idan har ana son samun kyakkyawar makomar dan Adam, to ya kamata a yi kokarin ba da muhimmanci da ma tabbatar da lafiyar jama’a. Kuma a yayin da daukacin bil-Adam ke fuskantar matsalar kiwon lafiya, hadin gwiwa ce hanya mafi dacewa wajen yaki da cutar da tabbatar da lafiyar kowa da kowa a duniya。Sanin kowa ce cewa, sai da lafiya ake iya komai.
Idan aka nazarci wannan takardar bayani da idon basira za a ga cewa, wata babbar manufa da aka nuna, ita ce ba da muhimmanci ga jama’a da muradunsu, gami da ceto rayukan jama’a ba tare da tsimin kudi ko albarkatu ba. Hakika wannan manufa, ita ce fasaha mafi muhimmanci da kasar Sin ta samu, a kokarinta na neman shawo kan cutar, kuma bayan watanni 3 ana gudanar da aiki ba dare ba rana, kwalliya ta biya kudin sabulu. Masu hikimar magana na cewa, sai an zubar da Ruwa a kasa kafin a taka Damshi. Sinawa baki daya sun hada kai sun jajurce, kuma daga karshe sun cimma nasara a dukkan fannoni.
Manufar ba da muhimmanci ga jama’a na nufin, a rika ba da cikakkiyar kulawa kan muradun da ya shafi jama’a, da dogaro kan jama’ar kasar da hadin gwiwa tare da su a kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nanata muhimmancin kula da rayuka da lafiyar jama’a. Bisa wannan umarnin da ya bayar ne, aka yi ta kokarin neman kwararrun likitoci, da na’urori masu inganci, da sauran albarkatun da ake bukata, don kyautata aikin jinyar wadanda suka harbu da cutar.
A fannin farfado da tattalin arziki ma haka lamarin yake, wato ana dogaro kan jama’a domin kowa ya ba da gudunmawa a kokarin maido da harkokin kasuwanci da masana’antu a kasar, don tabbatar da kare muradun dukkan al’ummun kasar.
Hakan ya karfafawa Sinawa gwiwa na cimma duk wani buri da suka sanya a gaba a fannin raya kasarsu, da tabbatar da makoma mai haske a kasar, gami da samar da gudunmawa ga yunkurin raya tattalin arzikin duniya baki daya. Kowa ya yi da kyau zai ga da kyau. (Ibrahim Yaya daga CRI Hausa)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: