Sake Fasalin Kasa: Gwamna El-Rufai Ya Yaba Da kokarin Hon. Garba Datti Babawo 

Sabon Gari

Daga Bello Hamza,

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya jinjina wa ‘yan majalisar kasa biyu daga jihar Kaduna bisa kokarin su na kafa dokar da za ta samar da cikkaken kasa mai bin tafakin tarayya kamar yadda kwamitin jam’iyyar APC na ‘True Federalism Committee’ ta bayar da shawara.

Ya godewa Sanata Uba Sani da Hon. Garba Datti akan yadda suka nuna wa duniya cewa, majalisar kasa ita ce kadai wajen da za a kafa dokokin da za su sauya fasalin kasar na ana ne kuma ake da ikon kafa dokokin da za su tabbatar da jadawalin mulki ga sauran bangarorin gwamnati.

Gwamna Malam El-Rufai ya kuma yi fatan sauran ‘yan majalisa za su yi koyi da wadanna ‘yan majalisar daga jihar Kaduna ta hanyar daukar nauyin samar da dokokin da sauya fasalin kasar a cikin ruwa sanyi.

Gwamnan ya ce, dokoki hudu da Sanata Uba Sani ya jagoranci kafawa wadda ta nemi a sauya fasalin yadda rundunar ‘yan sandan kasar nan ke tafiya, tana da matukar mahimmanci kwarai da gaske, haka kuma dokar da Hon. Garba Datti ya jagoranci kafawa a majalisar wakilai wadda ta shafi harkar kungiyar kwadago da kuma yadda zjihohi za su fuskanci biyan mafi karanci albashi ga ma’aikatansu wani mataki ne mai mahmanci a harkar rarraba karfin mulki a kasar nan.

Gwamnan ya bayyana wannna yabon ne a takardar sanarwar da jami’in wasta labaransa, Muyiwa Adekeye ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai a Kaduna, Gwamna ya kuma nemi sauran ‘yan majalisar su yi koyi da jajircewa irin na Hon Datti Babawo na bayar da wakilici na gari.

Exit mobile version