• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sallar Idi Babbar Rana Ga Musulmi

by Nuhu Ubale Ibrahim
2 years ago
Sallar Idi

Da sunan Allah mai Rahama mai Jin ƙaai. Yabo da godiya da kirari da girmamawa sun tabbata ga Allah Shi kaɗai. Yabon Allah da amincinsa su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta, shugaban na farko da na ƙarshe tare alayensa da sahabbansa baki ɗaya. 

Bayan haka;
wannan rubutu ya ƙunshi bayani akan sallar idi a bisa fahimtar Mazhabar Malikiyya. Ga bayanin kamar haka:

  • Layya Babbar Ibada: Yadda Ake Gudanar Da Ita Da Matsayinta A Musulunci
  • Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1

1. Sallar idi sunna ce mai ƙarfi ta wajibi.

2. Liman da mamu za su tafi filin idi bayan rana ta fito domin suna isa filin idi hantsi ya yi sai a yi salla.

3. Ana yin sallar idi a filin idi ba a masallaci ba sai dai idan akwai lalura, to za a iya yi a masallaci, haka nan waɗanda suke a garin Makka za su yi ta ne a Harami.

LABARAI MASU NASABA

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

4. Mustahabbi ne mutum ya yi wanka domin sallar idi.

5. Mustahabbi ne idan an yi wankan a tafi masallaci ba tare da ɓata lokaci ba.

6. Mustahabbi ne a yi ado a sanya turare da sababbin tufafi ga wanda yake da iko.

7. Za a tafi filin idi ana kabarbari a bayyane har a je filin idi, idan an je ba a yin nafila za a zauna a ci kaba da kabarbari har liman ya ƙaraso, sai a tsaya da kabarbari. Idan liman yana kabarbari , nan ma mamu za su yi kabarbari idan liman ya yi.

TAMBIHI: Kabarbari aka fi buƙata sama da wazi kafin liman ya zo, don Allah a bar al’umma su raya kabarbarbari a wurin idi.

8. Sallar idi raka’a biyu ce, kuma ana yin karatu a bayya ne, a raka’a ta farko ana yin kabbara bakwai har da kabbarar harama sai liman ya fara karatu, a ta biyu kuma kabbara shida har da ta mikewa. Ana karanta Fatiha da Sabbi a rakar farko a ta biyu kuma Hal’ataka ko kuma makamantansu.

9. Idan mutum bai riski wani abu tare da liman da bai aka’a ba, to, zai yi kabbara bakwai a raka’a ta farko kafin ya yi karatu, kuma zai kabbara shida a raka’a ta biyu kafin ya fara karatu kamar yadda liman ya yi.

10. Ba a yin nafila bayan an gama sallar idi.

11. Liman zai yi huɗuba guda biyu kuma zai zauna a tsakaninsu kuma ana so ya yawaita kabarbari a huɗubarsa.

12. Ana so a yi sallar layya da wuri akan ta sallar azubi, domin ana so a ci abinci kafin a tafi karamar salla, ita kuma ta layya sai bayan an dawo.

13. Kabarbari da ake so a yi, laffuzansu suna da yawa kuma za a iya yin kowanne, daga ciki akwai: Allahu Akbar Allahu Akbar La’ilaha illallahu Allahu Akbar Allahu Akbar Walillahil Hamdu.

14. Ana so a rinƙa kabarbari a bayan kowacce salla ya farilla sau uku bayan salla da kwana uku, kuma ana so a yawaita zikiri a cikinsu.

15. Mustahabbi ne ga mata da yara idan ba za su je sallar idi ba, to su yi wanka da ado da sanya sababbun kaya idan da hali.

16. Mata su guji caba ado da sanya turare idan za su idi saboda gudun fitina.

17. Makruhi ne mutum ya ƙi yin ado da kwalliyya da gayu a ranar idi wai don gudun duniya, idan kuma ya ƙi yi da sunan addini, to ya zama ɗan bidi’a.

18. Yara da mata za su iya yin wasanni a ranakun idi.

19. Mustahabbi ne mutum ya sabunta hanya wajen dawo gida, watau ya sauya hanya.

Allah ya karɓa mana ibadunmu ya gafarta mana. Amin.

Nuhu Ubale Ibrahim
Abu Razina Paki
Zul-hijja 9,1444H

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka
Bakon Marubuci

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
gombe
Ilimi

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Ilimi

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
Next Post
Shugabancin Nijeriya Na Da Matukar Wahala -Buhari

Shugabancin Nijeriya Na Da Matukar Wahala -Buhari

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

November 8, 2025
Majalisa Na Binciken Kwangilar Titin Naira Biliyan 1.46 Da Aka Yi Watsi Da Shi A Kaduna

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

November 8, 2025
Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

November 8, 2025
An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

November 8, 2025
An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

November 8, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.