Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu na Girki Adon Mata.
Abubuwan da Uwargida za ta tanada:
Beradi, salad, tumatur, kokumba, ham, kecof.
Da farko uwargida za ki samu biredinki mai yanka-yanka sai ki dakko tusta ki yi tostin dinshi ba tare da kin sa masa komai ba, idan ya dan gasu sama-sama sai ki kwashe shi, sannan ki dakko tumatur ki wanke shi ki yayyanka shi a kwance rawun kenan, sai ki ajiye shi a gefe, sannan Kokumbar ki wanke ta itama ki yayyanka ta, sai salad ki wanke shi amma ba za ki yanka shi ba, sai ki dakko wannan biredin da kika gasa ki shinfida salad din a sama sannan ki jera tumatur din a saman salad sai Kokumba itama ki jera ta a saman tumatur din, sai ham din shima ki dora shi a samansu, sannan ki barbada kecof din a saman su gaba daya sai ki rufe da dayan biredin, shi kenan ya kammala. A ci dadi lafiya gaskiya akwai dadi sosai.
Wani Hadin Kuma:
Bambancin sa da wannan shi ba da salad da tumatur da kokumba ake hadawa ba:
Uwargida za ki samu biredi, ciz, food coloring,
Yadda za ki hada shi:
Da farko za ki samu hat shaif sai ki cire tsakiyar biredin da shi ki ajiye a gefe, sannan ki yi giretin ciz din shima ki ajiye shi a gefe, sai food coloring ki samu kamar raibo kalos da shi za ki yi amfani sai ki raba wannan ciz din da kika yi giratin yawan food colouring kamar kala biyar, kowanne ki kwaba shi da kala daya, girin, faful, ja, ruwan goro, shudi, sannan ki dakko wannan biredin da kika yi hat dinshi sai ki diba kowane kalo kina jerawa a saman hat biredin sai ki dakko wani hat ki rufe haka za ki yi har ki gama. Sannan ki sa su a wofuls meka sai ki rufe ki barshi ya gasu.
Akwai dadi sosai idan kina so ki yi gayu za ki iya jera shi a tire amma kafin ki fara dora shi a tire sai ki samu salad ki wanke amma kar ki yanka sai ki shimfada shi a saman tiran sannan ki jera su yana kyau sosai.