Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RA'AYI

Sanata Ali Ndume: Dan Siyasa Mai Tagomashin Da Ya Dade Yana Jan Zaren Sa

by Tayo Adelaja
September 19, 2017
in RA'AYI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Sanata Mohammed Ali Ndume yana daga cikin rikakkun yan siyasar yankin arewa maso-gabas, wanda tauraruwar ta haskaka a siyasar Nijeriya, ya jima yana jan-zaren sa a fagen, mutum ne wanda yake da tasirin gaske a siyasar jihar Borno. Mutum ne jajirtacce dangane da inda yasa gaban sa. Mutum ne wanda ya dade ana gwagwarmayar rayuwa da fadi-tashi tun a cikin kuruciyar sa ta dandali, makaranta, wuraren aikin gwamnati da a siyasance.

samndaads

Sanata Ali Ndume shi ne yake wakiltar al’ummar kananan hukumomin Bi’u, Kwaya-kusur, Dambuwa, Chibok, Howel, Bayo, Askira-uba da mahaifar sa Gwaza dake kudancin jihar Borno a zauren malisar dattijan Nijeriya.

An haifi Sanata Mohammed Ali Ndume ne ranar 20 ga watan Nuwambar shekarar 1959 a garin Gwoza dake jihar Borno. Ya fara karatun sa na firamari ne a makarantar Gadamayo dake Gwoza inda ya kammala a 1972. Ndume ya zarce zuwa makarantar sakandire ta kimiyya dake Mubi, can baya Gongola(Adamawa yanzu). Ali Ndume mutum ne mai hazaka, juriya da kazar-kazar na jagoranci, lokacin da yana dalibi ya jagoranci dalibai a mukamai daban daban, tun a matakin sakandire.

Malami a Ramat Polytechnic, wanda a shekarar 1988, ya sami tallafin karatu a cibiyàr bada tallafin karatu da kasar Amurikà (USAID), inda yayi kwas na share-fage a fannin kasuwanci da ilimin na’ura mai kwakwalwa a jami’ar Toledo Ohio, ta Amerika tare da kammala shaidar karatun  Digiri na daya(B.Ed) dana biyu( M.Ed) a shekarar 1990. Har wala yau kuma ya taba samun kyautar yabo ta Magna Cum Laude; ta kwararru.

Daga bisani ya dawo Nijeriya don ci gaba da aikin sa na koyarwa a Ramat Polytechnic Maiduguri, Borno har zuwa 2003, inda ya tsunduma fagen siyasa gadan-gadan, inda ya shiga da kafar dama.

Mohammed Ali Ndume a jam’iyyar ANPP: A shekarar 2003 ne aka zabi Hon Mohammed Ali Ndume domin ya wakilci al’ummar sa a kujerar mazabar Chibok/Damboa/Gwoza; a zauren majalisar wakilai, karkashin lemar jan’iyyar ANPP: matsayin da yake rike dashi har zuwa 2011. Yayin da kuma a shekara ta 2007 ya rike shugaban maras rinjaye a zauren majalisar wakilai ta zango na shida (6th), inda ya shiga da kafar dama a zauren majalisar tare da bude sabon shafi, kuma Ali Ndume ya taka muhimmiyar rawa a wannan matsayi nasa.

Jajircewar Hon Ali Ndume da fadi-tashin sa sun jawo masa farinjini da yin fice a tafarkin siyasa. Wanda daga bisani sabani ya shiga tsakanin sa da wasu jiga-jigan jam’iyyar sa a jihar Borno; a lokacin Ali Modu Sheriff ne gwamnan jihar. Matsalar ta taso ne a lokacin da ya nemi jam’iyyar tasa da ta bashi damar sake tsayawa takara, yayin da wannan bai samu ba daga jam’iyyar, sai al’ummar mazabar sa suka tilasta masa ficewa daga jam’iyyar ANPP zuwa PDP.

Ali Ndume a jam’iyyar PDP: A watan Disambar shekarar 2010; kimanin saura kwanaki 100 a gudanar da babban zaben 2011 Ndume ya canja sheka zuwa jam’iyyar PDP, tare da bayyana cewa abinda ya jawo daukar wannan matakin shi ne rashin adalcin da jam’iyyar ANPP. Dadin-dadawa kuma ya bayyana cewa yana da gagarumin goyon bayan jama’ar sa, dari bisa dari.

Ana kalon cewa dwowar Ali Ndume a jam’iyyar PDP ya rage karsashin tasirin jam’iyyar ANPP a kudancin jihar Borno. Dalilin kuma shi ne saboda yadda ya kasance babban jigo kuma mai tallafa mata a sha’anin kudi sannan da farinjinin da yake dashi a idon talakawan yankin, kana mai karfin fada aji a ilahirin siyasar yankin arewa maso-gabas.

Baya ga wannan babban kamu da PDP tayi a kudancin Borno, sai jam’iyyar ta bashi damar tsayawa kujerar majalisar dattawa a karkashin inwar ta, inda ta bukaci Alhaji Sanda Garba, wanda a lokacin shi ne zai tsayawa jam’iyyar takarar kujetar majalisar dattawa mai wakiltar kudancin Borno.

Sanata Ali Ndume ya taka mashahuran gudamawa wajen kudurori masu ma’ana ga al’ummar tasa dama kasa baki daya. Kudurorin da suka hada da dokar da ta amince a ware kason kudi ga mazabun yan  majalisa (Constituencies Debelopment Fundda) ta gyaran fuska ga dokar zabe (Electoral Act Amendment Bill) wadda ta ba yan gudun hijira Samar yin zabe a sansanonin su a zaben shekarar 2015.

A cikin wannan yanayi, Sanata Ali Ndume; shida wasu na kut-da-kut dashi suka rankaya daga jam’iyyar tasu zuwa sabuwar jam’iyyar APC wadda daga bisani ta kwace mulki daga hannun PDP, a babban zaben 2015.

Mohammed Ali Ndume ya sake darewa dodam kan kujerar sa ta majalisar dattijai, bayan zaben 2015 inda daga bisani kuma ya kasance shugaban masu rinjaye a zubin majalisar ta takwas (8th). Kananan huyankin sun

Hon Ali Ndume ya fuskanci barazana kala kala a kasancewar sa shugaban masu rinjaye a zauren majalisar, bisa ga wannan ya jawo tutsun wasu daga cikin yan majalisar jam’iyyar tasa ta APC Wanda kuma daga bisani suka tsige shi daga mukami nasa na shugaban masu rinjayen, ranar 10 ga watan Januwarin shekarar 2017, inda aka maye gurbin sa da Dukta Ahmed I Lawan daga jihar Yobe.

Har wala yau kuma, barazanar bata tsaya a nan ba, inda a cikin watan Maris na shekarar, majalisar dattijan ta dage Sanatan zuwa watanni shida. Ali Ndume ya fuskanci wannan tsattsauran matakin baya ga sakamakon kwamitin ladabtarwa a karkashin shugabancin Sanata Anyanwu ya mika rahoton sa, wanda ya bayyana samun sanatan da laifin da zauren ya zarge shi na shigowa da wata mota mai sulke kirar Range Rober da aka ce anyi sojan gona a takardun shigo da ita. Inda shi kuma Ali Ndume ya musanta wadannan zarge-zargen.

Kafin hakan, Sanata Ndume ya kara da bayyana cewa hatta zancen da ake kwarmatawa dangane da binciken a kafafen yada labarai ya ji su, sannan kuma ba a fito balo-balo da zai tabbatar shi ne abin ya shafa. Yayin da ya bukaci majalisar kan ta fito fili tare da warware zare da abawar zargin.

Bisa ga wannan mataki na dakatar da na tsawon watani shida, Sanata Ndume ya bayyana cewa bai ga dalilin da zai sa ya bada hakuri ko afuwar laifin da bai San ya aikata ba.

Haka zalika kuma, wannan matakin dakatarwa wanda majalisar dattibai ta dauka a kan sa ya jawo caccaka daga masana tsarin kundin dokokin kasar nan. Irin su dan rajin kare hakkin Bil Adama, Femi Falana SAN, Mr Taidi Jonathan, tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa a reshen ta dake Minna; an nakalto suna cewa an saba ka’ida wajen dakatar da Sanata Ali Ndume har na tsawon wata shida.

Masanan sun bayyana cewa yadda yake rubuce a kundin mulkin Nijeriya cikin sashe na 6 dana 6 a cikin baka; karamin sashen ‘a’ da ‘b’ na shekarar 1999 cewa ba a yarda a dakatar da dan majalisa tsawon lokacin da zai zarta kwanaki 14 ba. Inda kuma suka yi kakkausan suka dangane da wannan matakin da suka kira baya kan ka’ida.

Muhimmancin wannan dan taliki ga al’ummar sa dama a siyasar yankin arewa maso-gabas ya jawo gwamnan jihar Borno; Hon Kashem Shettima ya jagoranci wata kakkarfar tawaga zuwa zauren majalisar da ganawa da shugaban majalisar dattijan inda ya bukaci majalisar da ta janye wannan dakatarwa da ta yiwa Sanata Mohammed Ali Ndume. Amma Bokola Sarakin ya kekasa kasa ya ce bashi da hurumin canja wannan matsayar.

Ali Ndume mutum ne wanda al’ummar mazabar da ke matukar girmama shi, musamman bisa kokarin fadi-tashin kyautata rayuwar su. Wannan a haka yake gudanar da mu’amalar sa a har a bayan majalisa ta dakatar dashi. A cikin yan kwanakin nan ma ya raba motoci kirar Bolkswagen Golf dari uku (300) ga matasan Gwoza domin rage zaman kashe wando, da bunkasa tattalin arzikin jama’ar yankin sa.

SendShareTweetShare
Previous Post

Jihar Yobe Na Sahun Gaba A Yawaitar Masu Luwadi –Alhaji Bukar Modu

Next Post

Gwamna Bagudu Ya Je Ta’aziyar ’Yan Nijar Da Ruwa Ya Cinye

RelatedPosts

Hon. Bello

Abinda Ya Sa Hon. Bello Kumo Ya Ciri Tuta A Siyasar Gombe

by Sulaiman Ibrahim
6 days ago
0

Irin girman tasirin da Jagorori suke yi a fannonin rayuwa...

Sabuwar Shekara

Wata Mahanga Daga Jawabin Buhari Na Sabuwar Shekara

by Muhammad
3 weeks ago
0

Daga Gidado Ibrahim, Jigo a tsarin shugabanci na Dimokradiyya shi...

Yadda Cin Zarafi Ke Neman Zama Dabi’ar Wasu ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Ta Jihar Kano

Yadda Cin Zarafi Ke Neman Zama Dabi’ar Wasu ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Ta Jihar Kano

by Daurawa Daurawa
3 weeks ago
0

Daga Usman Suleiman Sarki Mulkin dimokaradiyya tsari ne da ya...

Next Post

Gwamna Bagudu Ya Je Ta’aziyar ’Yan Nijar Da Ruwa Ya Cinye

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version