Sarkin Saminaka Ya Bukaci A Fitar Da Kayan Abinci Ga Talaka

Saminaka

Daga Isah Ahmed

Mai martaba Sarkin Saminaka da ke jihar Kaduna, Alhaji Musa Muhammad Sani, ya yi kira ga gwamnatocin kasar nan, su fitar da kayan abincin da su ka ajiye, su rabawa talakawa. Domin rage radadin mawuyacin halin da su ke fama da shi, na rashin abinci. Sarkin ya yi wannan kira ne, a lokacin da ya ke jawabi a wajen taron bikin Maulidi, da a ka gudanar a garin Saminaka a ranar alhamis din nan.

Sarkin ya yi bayanin cewa daukar wannan mataki, ya zama wajibi ganin irin abin da ya faru, a yan kwanakin nan, inda talakawa su ka rika fasa wuraren da a ka ajiye abinci, a kasar nan.

Ya yabawa al’ummar yankin Saminaka, kan yadda basu shiga wannan al’amari na fashe fashen wuraren da a ka ajiye, abinci ba.

Ya yi kira ga shugabannin addini, su cigaba da yin addu’o’i, domin addu’a ce kadai magannin dukkan matsalolin da su ke damun mu, a kasar nan.

Exit mobile version