Mai martaba Sarkin Zazzau, Mal. Ahmed Nuhu Bamalli, ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su ƙara duƙufa wajen gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya da kwanciyar hankali gami da yin addu’ar neman kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar nan.
Sarkin wanda ya yi wannan kiran a yayin bikin baje kolin al’adun gargajiya na shekara-shekara da Masarautar Kaltungo ta jihar Gombe ta saba shiryawa, ya kuma neman ƙarin addu’o’i wa gwamnatoci domin samun nasarar sauƙe nauyin da ke kawukansu wajen shawo kan matsalolin da ake fuskanta a ƙasar nan.
- Tarihin Katsina Daga Karni Na Goma
- Cire Tallafin Mai: Magani Mai Daci Ga Kashi 99 Cikin 100 Na ‘Yan Nijeriya
Nuhu Bamalli wanda shi ne uban taron, ya ce, babu wata ƙasa da za ta cigaba ba tare da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba, don haka ne ya nemi jama’a da su kauce wa shiga dukkanin wani abun da ka iya janyo matsala ga zaman lafiyar ƙasa.
Ya kuma yaba wa Sarkin Kaltungo, Injiniya Sale Muhammadu Umar da ya kasance mai shirya taron da ke ƙara haɗa kan al’ummar masarautarsa da kuma yadda yake nuna damuwa wajen cigaban al’ummarsa haɗi da kiyaye tarihi da al’adun masarautar.
Shi kuma a nasa jawabin, gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bada tabbacin gwamnatinsa na cigaba da kiyaye rayuka da dukiyar al’ummar jihar tare da bada gagarumin gudunmawa wajen bunqasa al’adun da jihar ke da su.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Manasseh Daniel Jatau, ya hori jama’a da a kowani lokaci su kasance masu mutunta sarakuna da al’adun gargajiya domin kyautata cigaba mai ɗaurewa.
Shi kuma a nasa ɓangaren, shugaban taro, Hon. James Joseph Damara (Kauran Kaltungo), ya gode wa irin shugabanci na kwarai da sarkin Kaltungon ke yi wajen kasancewa uba ga kowani ɗan masarautar haɗi da ‘yan uwanta da ke ƙara kyautata zaman lafiya a tsakanin al’ummar masmasarautar.
Ya ce, muhimmancin al’ada baya misaltuwa, yana mai cewa, a bisa mutunta al’ada ne manyan baƙi suka fito daga sassa daban-daban domin halartar wannan taron a Kaltungo, ya misalta sarkin garin a matsayin wani jarumin da ke da buƙarin haɗa kan jama’a da bunqasa al’adu da zaman lafiya a kowani lokaci.
A bikin dai wanda sarkin ya saba gudanarwa, ana baje kolin al’adun gargajiya da raye-raye gargajiya haɗi da baje nau’ikan kalolin abinci da ake da su a masarautar Kaltungo da ma makwafta, inda kowace ƙabila ke fitowa ta nuna asalin al’adarta da ke zama gwanin sha’awa ga mahalarta taro.
Taron wanda ake shafe kusan mako gudana a na gudanarwa, sarkin na kuma shirya taron liyafa na musamman wa ‘yan jarida da sarakuna da sauran manyan baƙi.
A wajen liyafar da sarkin ya shirya wa ‘yan jarida, tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jarida na jihar Bauchi, Malam Ibrahim Muhammad Malamgoje, ya yi kira ga masu hannu da shuni ko gwamnati da su kafa wata gidan rediyo ko talabijin a ƙaramar hukumar Kaltungo lura da yadda sarkin ke so da qaunar ‘yan jarida haɗi da mutunta aikin nasu.
A cewar Ibrahim wanda wakilin RFI Hausa ne, a dukkanin yankin arewa babu wani sarkin da ke gayyatar ‘yan jarida daga sassa daban-daban na ƙasar nan kawai domin ya zauna da su ya shirya musu ƙasaitaccen liyafa haɗi da jinjina wa irin qoqarin da suke bayarwa wajen cigaban ƙasa.
A nasa ɓangaren, Sarkin Kaltungo, ya ce, ‘yan jarida na da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen cigaban ƙasar nan, don haka akwai buƙatar a kasance ana jinjina wa irin ƙoƙarinsu a kowani lokaci. Kazalika ya kuma yaba wa irin ƙoƙarin jami’an tsaro su.
Ita kuma jigon taron, Hajiya Sa’adatu Saad Mustapha, ta ce, a kowani shekara ‘yan jarida sun kasance masu tallata irin al’adu da masarautar ke da su, don haka ne ta nuna ‘yan jarida a matsayin abokan jere.