ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Saudiyya Ta Damke Bakin Haure Sama Da 16,000

by Sadiq
3 years ago
Saudiyya

Hukumomin Saudiyya sun ce sun kama bakin haure 16,407 da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba, a yankuna daban-daban cikin mako daya.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar na cewa an kama mutanen ne bayan wani samamen hadin gwiwa da jami’an tsaro suka kaddamar a sassa daban-daban cikin wannan wata na Ramadan.

  • Gobara Ta Tashi A Wani Kamfani Da Ke Jihar Legas
  • Falala Da Takawar Da Azumin Ramadan Ya Kunsa

Kamen ya hadar da mutunen da suke zaune a kasar ba tare da izini ba, da mutunen da ba su da takardun shiga kasar, sai kuma mutunen da suka saba ka’idojin aiki na Saudiyya.

ADVERTISEMENT

Ma’aikatar ta ce ta kama wasu a lokacin da suke kokarin tsallaka kan iyakar kasar, wasu kuma an kama su ne lokacin da suke yunkurin fita daga kasar.

Ta ce kashi 74 na waɗanda aka kama, ‘yan Habasha ne, sai kashi 22 ‘yan asalin Yemen, kashi hudu kuma na sauran kasashe.

LABARAI MASU NASABA

EU Ta Koka Da Yadda Yaduwar Ta’addanci A Sahel Ke Barazana Ga Tsaron Turai

Trump Ya Caccaki Kasashen Turai Bayan Ayyana Nahiyar A Matsayin Mai Rauni

Ma’aikatar cikin gidan ta ce an tura ‘yan ci-rani 6,251 zuwa ofisoshin jakadancin kasashensu da ke Saudiyya don samar musu takardun izini, yayin da za a mayar da mutum 10,156 zuwa kasashen da suka fito.

Ta dai gargadi duk wani mutum da ya yi sanadin shigar da wani bakon haure cikin Saudiyya ba bisa ka’ida ba, ko ya ba shi masauki, ko aiki, da dai duk wani nau’in taimako – ya tabbatar cewa zai fukanci hukuncin da zai iya kai wa daurin shekara 15 a gidan yari, matukar aka kama shi.

Sannan da biyan tarar riyal miliyan daya, idan aka same shi da laifin hada baki wajen shigar da bakin haure cikin kasar, da kuma samar musu masauki.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

EU Ta Koka Da Yadda Yaduwar Ta’addanci A Sahel Ke Barazana Ga Tsaron Turai
Kasashen Ketare

EU Ta Koka Da Yadda Yaduwar Ta’addanci A Sahel Ke Barazana Ga Tsaron Turai

December 14, 2025
Trump Ya Caccaki Kasashen Turai Bayan Ayyana Nahiyar A Matsayin Mai Rauni
Kasashen Ketare

Trump Ya Caccaki Kasashen Turai Bayan Ayyana Nahiyar A Matsayin Mai Rauni

December 14, 2025
Rwanda Ta Musanta Hannu A Rikicin Da Ya Barke A Kibu Da DR Congo
Kasashen Ketare

Rwanda Ta Musanta Hannu A Rikicin Da Ya Barke A Kibu Da DR Congo

December 14, 2025
Next Post
Firaministan Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Singapore

Firaministan Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Singapore

LABARAI MASU NASABA

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.