Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Faisal bin Ibrahim Al-Ghamdi, ya ce Saudiyya ta kashe dala biliyan 100 domin sabunta da kuma faÉ—aÉ—a Masallatan Harami na Makkah da Madina.
Ya bayyana cewa an yi hakan ne don rage cunkoso, amfani da fasahar zamani, da kuma ƙara yawan mahajjata da masu yin Umara da za su iya ziyartar ƙasa mai tsarki a kowace shekara.
- An Watsa Shirin Fadakarwa Na Shagalin Murnar Bikin Bazara Na CMG A Masar
- Ana Sa Ran Bude Sabon Babin Raya Dangantakar Sin Da Amurka
Jakadan ya yi wannan bayani ne yayin da ‘yan Nijeriya 20 da aka yi wa gayyata ta musamman Æ™arÆ™ashin shirin Sarki Salman Bin Abdul’aziz Al-Saud ke shirin tafiya Umara kyauta.
Shirin masarautar Saudiyya na É—aukar nauyin masu zuwa Umara daga sassa daban-daban na duniya da ya haÉ—a da waÉ—annan ‘yan Nijeriya a wannan karo.
Jakadan ya kuma roƙi waɗanda suka samu wannan damar su kiyaye dokokin ƙasar da kuma bin ƙa’idojin hukumomi.
Al-Ghamdi ya ce Saudiyya za ta ci gaba da hidimtawa baƙin Allah cikin tsari da jin daɗi.