Musa Ishak Muhammad" />

Sharhin Fim Din “Kanwar Matata”

Daga: Musa Ishak Muhammad.

Suna: Kanwar Matata.

Tsara labari: Jamilu Ahmad Yakasai. 

Kamfani: ALMUBARAK International Films..

Daukar Nauyi: Almubarak International Films.

Shiryawa: Jamilu Ahmad Yakasai.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Jamilu Ahmad Yakasai, A’isha Aliyu Tsamiya, Maimuna Muhammad, Asama’u Sani, Baba Karami, Ahmad A. Bifa, Gali Ibrahim, Amal Umar da sauransu.

Fim din Kanwar Matata fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani mutum mai suna Anas (Jamilu Ahmad Yakasai) da matarsa Asama’u (A’isha Aliyu Tsamiya) da kuma kanwar matarsa Mufida (Amina Amal). Shi dai Anas ya samu kansa ne a cikin mawiyacin hali bayan kanwar matarsa wato Mufida ta dage cewa, ita fa ta kamu da tsananin kaunarsa, kuma ita so take ya aure ta duk da cewa kuwa yana auren yayarta ne.

A farkon fim din an nuno Asama’u tana kwance da daddare tana bacci, sai ta farka amma ba ta ga mijinta Anas a gefenta ba.A nan ne ta taso tana zuwa sai ta same shi yana zaune a falo yana waya. A lokacin wata ce wadda shi kansa bai san kowacece ba ta kirawo shi tana shaida masa cewa tana kaunarsa kuma ba ta da wani buri illa auren sa. A nan take ya sanar da ita cewa hakan sam ba abu bane da zai yiwu ba. Yana cikin ba ta amsa ne sai ga matarsa ta shigo falon, da ya ji ta taho sai ya kashe wayar, sai take ce masa me ya sa za ka kashe wayar dan ka gan ni? Ai ka ci-gaba da wayarka kawai. A nan Ya yi ta kokarin yi mata bayani amma ina sam bata fahimce shi ba, wanda a karshe ma ta yanke jiki ta fadi a sume. A nan take aka dauke ta sai asibiti inda anan ne Likita ya ke fada wa Anas cewa lallai matarsa tana cikin mawiyacin hali, kuma indai ana son rayuwarta to fa sai an nisance ta da duk wani abu da zai ringa tayar mata da hankali.

A daya bangaren kuma ita wannan mai kiran Anas ba ta daina kiransa tana sanar da shi irin soyayyar da take masa ba, haka dai ya yi ta kaffa-kaffa saboda kar Asama’u ta san halin da ake ciki. Yana cikin wannan halin ne, shi ne abokinsa ya ba shi shawarar cewa ai ya kamata ace sun hadu da ita mai kiran nashi domin sai sun hadu ne za a iya sanin ta ya ya za a bullowa da matsalar. Anas sai ya dauki wannan shawarar kuma sai suka saka rana da lokaci akan za su hadu da ita a ofis dinsa da misalin karfe uku na rana.

Da misalin karfe uku na rana kuwa chan sai ga Mufida wato kanwar Asama’u matar Anas ta shigo ofis din Anas, shi ne yake tambayar ta mai ta zo yi har ofis haka,sai ta ce na zo ne na cika alkawarin da muka yi cewa za mu hadu karfe uku na rana a nan. A nan ne fa Anas ya cika da mamaki har yake tambayar ta daman ke ce ki ke kirana a waya? Sai kuwa ta bude baki ta ce ita ce, sannan ta fara bayyana masa irin yadda ta kamu da sonsa da kuma irin mawiyacin halin da ta ke ciki a kan soyayar tasa. A nan fa Anas ya fara yi mata fada yana cewa da ita wannan ba fa abu ne mai yiwuwa ba ko kadan. Kin amincewar Anas ga bukatar Mufida shi ne fa ya saka ta cikin mawiyacin hali, a koda yaushe ba ta da abun yi sai kuka da tunani. Amma kuma ta ki fadawa kowa halin da take ciki, hatta iyayenta wato Alhaji (Baba Karami) da kuma Mamanta (Asama’u Sani) ma taki sanar da su damuwarta.

A haka dai Anas ya ci-gaba da rayuwa cikin matsi da kuma takurawar Mufida agareshi amma kodayaushe yana yin kaffa-kaffa, kuma yana sirrinta abun saboda kada matarsa ta ji ciwonta ya tashi. Da abun ya fara yi wa Anas yawa ne fa, shi ne ya yanke shawarar zuwa ya sanar da Alhaji wato mahaifin Mufida da Asama’u, ya sanar da shi duka abunda yake faruwa sannan ya nemi alfarmar kada a bari Asama’u ta san halin da ake ciki. A nan ne iyyayen Mufida suka kirawo ta suna mata fada kuma aka nuna mata abinda ta dakko ba mai yiwuwa bane.

A haka Mufida ta ci-gaba da rayuwa cikin tsanin ciwon son Anas, wanda hakan ya tilasta kai ta asibiti sakamakon hawan jini da ya same ta da kuma ciwon zuciya da yake shirin kamata. A sakamakon haka ne likita ya bada umarnin cewa fa indai ana son rayuwar Mufida to fa dole ne sai an bata abinda take so. Duba da ana dab da iya rasa rayuwar Mufida, haka ne ya sa mamanta ta ce to fa gaskiya ba za ta zuba ido tana ji tana gani ta rasa ‘yarta ba. Shi ne take fadawa Alhaji cewa koma ta ya ya ne ta shirya nemowa ‘yarta maganin damuwarta. Ta ke  fada masa cewa za ta bayyana sirrin da suka dade suna boyewa, waton ashe Asama’u ba ainihin ‘yarsu ba ce ta cikinsu, ita ‘yar mai aiki a gidansu ce wacca ta mutu a lokacin da ta haifi Asama’un.

Daga nan ne Maman Mufida ta tafi gidan Asama’u take fada mata gaskiyar lamari sannan take ce mata tana neman ta yi mata alfarma ta amince Anas ya auri Mufida domin ceto rayuwarta. Shi ne Asama’u take cewa ai ba za ta ki yi mata ko wacce iriyar alfarma ba, duba da irin yadda suka rike ta da amana da kyautatawa, babu banbanci tsahon shekaru masu yawa. A karshe dai Asama’u ta amince Anas mijinta ya auri Mufida, sannan ta nemi alfarmarsa a kan da ya daure ya auri Mufida domin ceto ranta, sannan ya taimaka wa Asama’un wajen yi musu halacci,wanda daga baya shi ma ya amince cewa zai auri Mufidan.

ABUBUWAN YABAWA

Fim din ya samu aiki mai kyau.

Hotuna da sauti duk sun fita radau.

Jaruman sun dace da labarin.

Sunan fim din ya dace da labarin.

Labarin ya isar da sakon da ake bukata.

KURAKURAI

Rashin bayyana sunan wanda ya bada umarnin fim din,domin tun daga farkon fim din har karshe babu inda aka bayyana sunan wanda ya bada umarnin fim  din.

Fitowar da aka nuno Anas ya zo ya karbi mukulli a gurin wata, kwatakwata bai da alaka da wani sako da ake so a isar a fim din.

Bayyanar kawar Asama’u a karshen fim din kuskure ne,domin an haskota a baya amma ba a nuna akwai wata alaka a tsakaninsu ba.

Inda fim din ya kare, bai kamata a ce ya kare a nan ba.

KARKAREWA

Fim din Matar Kanina ya zo da abunda faruwarsa abu ne mai wahala. Saboda ita Mufida bata son cewa ba iyayenta ne suka haifi Asama’u ba, tunda kuwa haka ne me yasa zata bar zuciyarta har ta kamu da son Anas bayan ta san bazai taba yiwuwa ta aure shi ba matukar suna tare da Asama’u. Fim din ya samu aiki mai kyau,domin kurakurai basu da yawa a cikinsa

Exit mobile version