Babbar Alƙalin Alƙalan Jihar Kano, Dije Abdu-Aboki, ta sauya wa tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje sabon alƙali.
Tsohon gwamnan dai na fuskantar tuhuma ne tare da wasu mutane bakwai ciki har da matarsa Hajiya Hafsah Ganduje.
- Hisbah Ta Haramtawa Maza Masu Kiɗan DJ Shiga Wurin Shagalin Bikin Mata A Jihar Kano
- Sarkakkiyar Zargin Da Gwamnatin Abba Ke Wa Ganduje
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), ya ruwaito cewa ragowar waɗanda ake tuhuma sun haɗar da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash properties Limited, da kuma Safari Textiles Limited.
Kafin wannan sauyi dai ana gudanar da shari’ar ne a wata babbar kotu mai lamba 4, ƙarƙashin mai shari’a Usman Na’abba, amma yanzu ta koma babbar kotu mai lamba 7 ƙarƙashin mai shari’a Amina Adamu Aliyu.
Mai magana da yawun hukumar shari’a ta Jihar Kano, Baba Jibo-Ibrahim ne, tabbatar da wannan sauyi a yau Alhamis yayin wata tattaunawa da manema labarai.
Jibo, ya ce ofishin babban mai shari’ar yana da ‘yancin yin hakan bisa doka.
Ana tuhumar shugaban jam’iyyar APC da laifuffukan takwas da suka haɗa da cin hanci, almundahana, almubazzaranci da dukiyar gwamnati na biliyoyin Naira.
Sai dai kuma har bayan wannan sauyi ba a sanya ranar sauraren shari’ar ba a gaban Adamu-Aliyu.